Zargin da Ake Yi Ya Tabbata, Auren Fitacciyar Jarumar Nollywood Ya Mutu
- Jaruma Abiola Adebayo ta tabbatar wa duniya cewa aure ya kare tsakaninta da mijinta Oluwaseyi Akinrinde tun Afrilun 2024
- A yayin da ta kawo karshen jita-jitar da aka dade ana yadawa, jarumar Nollywood din ta ce sun amince za su ci gaba da kula da ɗansu
- Jarumar ta bayyana wa mutane cewa ta shafe watanni 14 tana zubar da hawaye a kusan kowanne dare tun bayan mutuwar aurenta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Fitacciyar jarumar Nollywood, Abiola Adebayo, ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa, inda ta tabbatar da cewa aure ya kare tsakaninta da Oluwaseyi Akinrinde.
Abiola Adebayo, ta shaidawa duniya cewa tun a watan Afrilun 2024 ne ta rabu da mijinta Oluwaseyi, amma duk da hakan, suna tarayya wajen kula da ɗansu.

Asali: Instagram
"Ni da mijina mun rabu" - Jaruma Abiola
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram ranar Talata, jaruma Abiola ta yi murnar zagayowar ranar haihuwar tsohon mijinta tare da bayyana mutuwar aurensu a hukumance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumar ta rubuta cewa:
“Barka da zagayowar ranar haihuwa, tsohon mijina kuma uban ɗana. Ina addu’ar rahamar Ubangiji ta lullube ka, Ubangiji ya ci gaba da yin riko da hannayenka.”
Ta ci gaba da cewa:
“Eh, kun ji da kunnuwanku! Ni da mijina mun rabu tun watan Afrilun bara, amma mun yanke shawarar yin tarayya wajen kula da ɗanmu cikin kwanciyar hankali.”
"Ina zubar da hawaye a kowane dare" - Jaruma Abiola
Abiola Adebayo ta yi wa masoyanta jawabi, tana mai cewa:
“Ga duk wanda ke jin haushina kan hakan, ina ba shi hakuri. Na so ace wannan auren ya dore, amma zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Don Allah ku cigaba da yi mana addu’a.”
Ta kuma bayyana irin azabar da ta sha cikin shekarar daya da ta gabata, inda ta ce ana ganin murmushinta ne kawai, amma ita kadai ta san hawayen da take zubarwa a sirrance.
“Yayin da nake kokarin faranta wa jama’a rai da rana, a hannu daya kuma matashin kai na ya kan jike da hawaye na kusan kowane dare, tsawon watanni 14 da suka gabata."
- Jaruma Abiola Adebayo.

Asali: Instagram
Martanin jama'a kan mutuwar auren jarumar
Masoya, abokai da abokan aikin jarumar sun cika sashen sharhi da saƙonnin goyon baya da karfafa gwiwar tasaboda ƙarfin halin da ta nuna.
Jarumar Nollywood, Regina Chukwu, ta yi martani da cewa:
“Biola… Ubangiji ya shiga lamarinki.”
Wasu kuma sun nuna tausayi ga jarumar, suka rika yaba mata saboda juriyar da ta nuna da kuma yadda ta magance wannan babin na rayuwarta ba tare da wani ya ji ba.
Abiola da mijinta sun samu karuwar ɗansu na fari a watan Afrilu 2023 ta hanyar tsarin 'surrogate', watau wata mata ce ta ɗauki ciki a madadinta.
Karanta sakon jarumar a kasa:
'Matsala da jaruman fim ke fuskanta' - Tuge
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jarumar Kannywood, Hafsat Tuge, ta tofa albarkacin bakinta kan yadda ake kallon jarumai mata a matsayin wadanda ba sa son zaman aure.
Hafsat Tuge, wadda aka fi sani da Amaryar TikTok, ta ce mata 'yan Kannywood na zaman aure cikin mutunci da biyayya, sabanin abin da wasu ke zato.
Da aka tambaye ta kan shirin aurenta, ta bayyana cewa aure yana da lokacin da Allah ya tsara masa, amma a yanzu ba auren ne gaban ta ba.
Asali: Legit.ng