Barau Ya Yi Takaicin Rasuwar 'Yan Wasan Kano, Ya Mika Tallafin N22m ga Iyalansu
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya kai ziyara ta’aziyya ga iyalan ’yan wasan 22 da suka rasu
- Ya bayar da tallafin Naira miliyan daya ga kowanne daga cikin iyalan mamatan domin rage musu radadin rashin nasu
- Sanata Barau, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da ya girgiza Najeriya da addua'ar Allah Ya masu rahama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya kai ziyara ta'aziyya ga iyalan ‘yan wasa 22 da suka rasu a wani haɗarin mota da ya faru ranar Asabar.
Mutanen da suka rasa yaransu da sauran yan uwa da abokan arziki sun tarbi Sanata Barau tare da tawagarsa a masallacin Juma’a na Gwagwarwa, a karamar hukumar Nasarawa a jiha Kano.

Asali: Facebook
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau ya tallafawa iyalan 'yan wasan Kano
Jaridar Punch ta ruwaito mai ba ba Barau shawara na musamman kan kafafen yaɗa labarai, Ismail Mudashir, Sanatan ya ce mutuwar yan wasan ta girgiza yan Najeriya.
Sanatan ya kuma sanar da bayar da tallafin Naira miliyan ɗaya ga kowanne daga cikin iyalan mamatan domin rage musu radadin wannan rashi.
Ya ce ba iyalan mamatan kawai rashin ya shafa ba, har da daukacin al’ummar jihar Kano da Najeriya gaba ɗaya.
Barau ya yiwa yan wasan Kano addu'a
Sanata Barau I Jibrin ya shaidawa iyalan yan wasan cewa ya kai masu ziyarar domin jajantawa da nuna masu cewa yana tare da su.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Mun zo ne domin bayyana alhinimu da jajenmu bisa wannan mummunan lamarin da ya jefa mu cikin rashi da ba za a iya maidowa ba.”
Mun karbi wannan a matsayin ƙaddarar Allah. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta musu, ya azurta su da Aljannatul Firdausi, kuma ya ba ku juriya da haƙuri wajen jure wannan babban rashi.”
A cewar sanarwar, Sanata Barau ya samu rakiyar karamin Ministan Harkokin Gidaje da Raya Birane na Ƙasa, Yusuf Atta.
Sai kuma Manajan Darakta na Hukumar Ci Gaban Arewa maso Yamma, Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji da tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan.
Sauran sun hada da Babban Sakataren sa, Farfesa Muhammad Ibn Abdullah, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, malamai da attajirai.
Gwamnati ta tallafawa iyalan 'yan wasan Kano
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayar da tallafin kuɗi ga iyalan 'yan wasan da suka rasu a hatsarin mota.
Mataimakin gwamnan Kano, Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya sanar da cewa za a ba kowanne daga cikin iyalansu Naira miliyan daya don rage radadin rashin.
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin za ta ci gaba da kula da lafiyar waɗanda suka jikkata a sakamakon hatsarin motar da ya ritsa da su a Dakatsalle.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng