An Yi Rashi: Mahaifiyar Fitaccen Malamin Izala, Sheikh Asadus Sunnah Ta Rasu
- Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yi wa mahaifiyar malamin izala, Sheikh Musa Asadus Sunnah rasuwa a ranar Litinin, 28 ga Afrilu
- An tabbatar da rasuwar mahaifiyar Sheikh Asadus Sunnah a shafin malamin na intanet, inda aka ce za a gudanar da jana’izarta a jihar Kaduna
- Wata sanarwa ta bayyana cewa za a gudanar da jana'izar da karfe 1:00pm, a masallacin Juma'ah na Musabaqah da ke Unguwar Kinkinau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Mun samu labarin rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah.
Sheikh Musa Asadus Sunnah malamin Izalah ne da ya yi shuhura a Najeriya da ma kasashen ketare a fagen wa'azi da tafsirin Al-Qur'ani mai girma.

Asali: Facebook
Mahaifiyar Sheikh Asadus Sunnah ta rasu
Wani matashi dan kungiyar Izala, @el_uthmaan ya wallafa batun rasuwar mahaifiyar Sheikh Asadus Sunnah a shafinsa na X da safiyar Litinin, 28 ga Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El Uthman ya bayyana cewa za a gudanar da jana'izar mahaifiyar fitaccen malamin da ta rasu da misalin karfe 1:00pm na ranar Litinin.
Ya shaida cewa za a gudanar da jana'izar a babban masallacin Juma'a na Musabaqah, da ke Unguwar Kinkinau, jihar Kaduna.
Sanarwar matashin dan Izalar ta ce:
"InnalilLaahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!
"Allah ya ji ƙan mahaifiyar Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah, wadda ta rasu. Za a gudanar da janazarta da karfe 1:00 na rana a Masallacin Juma'a na Musabaqah, Kinkinau, Kaduna.
"Allah Ya ji ƙanta, Ya sa yar Aljannah ce. Ameen!"
Duba sanarwar a kasa:
An roki jama'a sun sanya mahaifiyar malamin a addu'a
Shafin Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah na facebook ya tabbatar da rasuwar mahaifiyar malamin, inda Legit Hausa ta ci karo da bidiyo da ke bayanin rasuwar.

Asali: Facebook
A cikin bidiyon, an ga wani malami, da ba a iya gane sunansa ba har zuwa lokacin wallafa rahoton yana bayani kamar haka:
"Tare da dukkanin komawa ga Allah, muna sanar da 'yan uwa, cewa Allah madaukakin sarki ya yi wa mahaifiyar Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah rasuwa, a yau Litinin 28 ga watan hudu, 2025.
"Kuma muna sanar da su insha Allahu ta'ala, za ayi mata jana'iza a masallacin Musabaqah da ke Kinkinau, karfe 1:00 na rana, da azahar din nan.
"Don haka muna rokon wadanda ke nesa, da su sanya ta a addu'a, Allah ya gafarta mata, Allah ya yafe mata, Allah ya sa Aljannah makomarta."
Kalli bidiyon a kasa:
Asali: Legit.ng