Musulunci Ya Yi Rashi: Shugaban Majalisar Shari'a a Najeriya Ya Kwanta Dama
- Shugaban Majalisar Shari'a ta Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, ya rasu kamar yadda babban malamin Musulunci, Sheikh Daood Imran Molaasan, ya sanar
- Sheikh Hadiyatullah ya kasance fitaccen malami daga Iwo a jihar Osun, wanda ya yi suna wajen kare Shari'a da zaman lafiya tsakanin addinai guda biyu da ake da su
- Ya shugabanci Majalisar Shari'a ta Najeriya tsawon shekaru, yana jan ragamar kungiya ta hanyar kalubale da cigaba da hadin kan al’umma domin samun zaman lafiya
- Sheikh Molaasan ya roki Allah SWT ya gafarta masa, yana mai jaddada cewa rasuwarsa ta bar babban gibi a shugabancin addinin Musulunci a Najeriya gaba daya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Shari'a ta Najeriya (SCSN), Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, ya yi bankwana da duniya.
An sanar da rasuwar marigayin ne a jiya Litinin 28 ga watan Afrilun 2025 ba tare da bayyana ranar da ya rasu ba ko kuma silar mutuwar malamin.

Asali: Facebook
Musulunci ya yi rashin babban malamin addini
Hakan na cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na 'The Grand Mufti of Yoruba Land'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban malamin Musulunci na Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan ya tabbatar haka a sanarwar da ya sanya wa hannu.
Sai dai bai bayyana inda marigayin ya rasu ko kuma ranar rasuwar tasa ba, kamar yadda sanarwar ta nuna.
Yadda Musulunci zai yi kewar marigayi Hadiyatullah
Sheikh Molaasan ya bayyana cewa rasuwar Sheikh Hadiyatullah ta bar babban gibi a fagen shugabancin Musulunci a fadin Najeriya.
Sanarwar ta ce:
"An haifi Sheikh Hadiyatullah a Iwo, wani gari da ke jihar Osun da ake alfahari da tarihin Musulunci.
“Sheikh Hadiyatullah fitaccen malami ne da ya yi fice wajen kare Shari’a cikin tsarin mulki da kuma tattaunawar addinai."

Asali: Facebook
Gudunmawar da marigayin ya bayar ga al'umma
Malamin ya ce kafin rasuwar marigayin, Sheikh Hadiyatullah ya shugabanci Majalisar Shari’a na tsawon shekaru, yana ba ci gaba a tsakanin al’umma muhimmanci.
Ya kara da cewa:
“Sheikh Hadiyatullah ya fara karatunsa a wajen malamai na gida, kafin daga bisani ya ci gaba da karatu a kasashen waje."
Molaasan ya kara da cewa marigayin ya sami karbuwa a fadin Najeriya da ma kasashen waje saboda zurfin iliminsa da salon shugabancinsa.
Ya kuma yi addu'a Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da Aljannatul Firdaus domin irin kokarinsa wajen hidimar addini.
Babban malamin addini kuma masanin hadisi, Dr. Bashir Aliyu Umar OON shi ne mataimakin Rasheed Hadiyatullah a majalisar.
Rufe makarantu: Majalisar shari'a ta goyi baya
A baya, kun ji cewa Majalisar shari'ar Musulunci ta Najeriya ta goyi bayan rufe makarantu a Ramadan, ta ce hakan zai taimaka wa dalibai wajen kare lafiyarsu daga tsananin zafi.
Majalisar ta bukaci jihohin Zamfara, Sokoto da Jigawa su ɗauki wannan mataki, tana mai cewa an dauki wannan shawara ne don amfanin addini da kiwon lafiya.
Ta ce gwamnatocin jihohi na da cikakken iko kan jadawalin makarantu, tana sukar masu adawa da matakin, ciki har da kungiyoyin Kiristoci a Najeriya da ta kalubalanci matakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng