Mainasara Habibi: Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Zariya, Tinubu Ya Aika Sako

Mainasara Habibi: Babban Malamin Musulunci Ya Rasu a Zariya, Tinubu Ya Aika Sako

  • Shugaba Bola Tinubu ya kadu da rasuwar Sheikh Mainasara Habibi, babban malamin Tijjaniyya da ya rasu yana da shekaru 67
  • Tinubu ya bayyana Sheikh Habibi Zariya a matsayin malami nagari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta ilimin addini
  • Shugaban ƙasar ya yi ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Kaduna, tare da yi wa Sheikh Habibi addu'ar samun rahama da gafara daga Ubangiji

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna tsantsar kaduwa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Mainasara Liman Habibi.

An rahoto cewa, Sheikh Mainasara Habibi ya kasance babban malamin darikar Tijjaniya a Zariya da ke jihar Kaduna, kuma ya rasu a karshen makon da ya gabata.

Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin Tijjaniya, Sheikh Mainasara Habibi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Hagu), Marigayi Sheikh Mainasara Liman Habibi. Hoto: @aonanuga1956, @BMB1_Official
Asali: Twitter

Sheikh Mainasara Habibi ya rasu a Zariya

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, wadda Legit Hausa ta samu, Shugaba Tinubu ya ce ya kadu da rasuwar malamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar, wadda Bayo Onanuga ya fitar da ita a ranar Litinin, 28 ga Afrilu, ta rahoto cewa Sheikh Mainasara Liman ya rasu yana da shekaru 67.

Onanuga ya ce babban malamin, kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban kwamitin masu wa'azi na kasa na Fitayanul Islam, da ke karkashin Tijjaniya.

Sanarwar Onanuga ta rahoto Shugaba Bola Tinubu yana cewa:

"Za a riƙa tunawa da Sheikh Habibi a matsayin malami nagari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta ilimin addini da hidima ga al'umma."

Tinubu ya yi ta'aziyyar Malam Mainasara Habibi

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa Sheikh Habibi, ya kasance mai yin wa'azin da ke mayar da hankali kan hadin kai tsakanin addinai, zaman lafiya da haɗin kan al’umma fiye da wa'azin da ke nuna bambance-bambancen ra’ayi.

Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Kaduna, majalisar masarautar Zazzau, da shugabannin ƙungiyar Tijjaniyya a Najeriya bisa wannan rashi.

Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma yi wa Sheikh Habibi addu'a, yana mai roƙon Allah ya gafarta wa malamin tare yi masa rahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.