Shugaba Tinubu Ya Kaɗu da Allah Ya Yi Wa Babban Sarki Rasuwa a Watan Ramadan

Shugaba Tinubu Ya Kaɗu da Allah Ya Yi Wa Babban Sarki Rasuwa a Watan Ramadan

  • Bola Ahmed Tinubu ya kaɗu bisa rasuwar shugaban Majalisar sarakunan Arewa a jihohin kudu kuma sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin
  • Shugaban ƙasar ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da al'ummarsa, yana mai bayyana cewa rashin basaraken babban rashi ne ga Najeriya
  • Basaraken ya rasu yana da shekaru 125 a duniya, kuma an yi jana’izarsa a karshen mako a yankin Sasa a ƙaramar hukumar Akinyele a Oyo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jimami da alhininsa kan rasuwar Sarkin Sasa, Haruna Maiyasin Katsina.

Marigayi Sarkin wanda ya fito daga jihar Katsina, ya kasance Shugaban majalisar sarakunan Arewa a jihohi 17 na kudancin Najeriya.

Bola Tinubu da marigayi sarkin Sasa.
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar sarkin Sasa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya yi alhinin wannan babban rashi ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin X mai ɗauke da sa hannun kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga.

Kara karanta wannan

Sarkin Sasa: Awanni da birne shi, an sanar da sabon basarake da zai maye gurbinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Sasa ya rasu ranar Asabar yana da shekaru 125 a duniya, kuma an yi jana’izarsa a karshen mako a yankin Sasa, da ke ƙaramar hukumar Akinyele a jihar Oyo.

A sanarwar, wadda mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa, Tinubu ya kaɗu da rasuwar sarkin Sasa.

Shugaba Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa rasuwar wannan fitaccen basarake babban rashi ne ga Najeriya baki daya, la'akari da irin tasirin da ya ke da shi.

A cewarsa, marigayi sarkin Sasa ya taka rawar ganin wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al'ummar ƙasar nan

Shugaban kasar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, al’ummar jihar Oyo da jihar Katsina, da kuma shugabannin ƴan Arewa da ke kudancin Najeriya.

Sarkin Sasa ya ba da gudummuwa sosai

Marigayi Alhaji Haruna Maiyasin ya kasance jigo a harkokin zamantakewa, inda ya zama ginshiki wajen daidaita alaka tsakanin ƴan Arewa da ƴan Kudancin kasar.

Kara karanta wannan

'Mun yi babban rashi': Gwamna ya girgiza da mutuwar sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin

A matsayin Shugaban Sarakunan Arewa a kudancin Najeriya, ya yi kokari matuka wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin kabilu daban-daban.

Sarkin Sasa.
Sarkin Sasa ya ba da gudummuwa wajen haɗa kan al'umma a Kudancin Najeriya Hoto: Alh. Kaseem Yaro
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya yi wa sarkin addu'a

Har ila yau, Tinubu ya jinjinawa kokarin marigayin na karfafa hadin kai da zumunci tsakanin ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban, yana mai cewa irin wadannan shugabanni na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.

"Rasuwar Sarkin Sasa babban rashi ne, domin ya kasance dattijo mai hangen nesa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummar Arewa da Najeriya baki daya," in ji Tinubu.

Shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma bai wa iyalansa da duk masu alaka da shi hakurin jure wannan rashi.

Gwamna ya yi jimamin rasuwar sarkin Sasa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya miƙa sakom ta'aziyya bisa rasuwar mai martaba sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin.

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake kuma shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohi 17 ya rasu

Ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayin da daukacin al’ummar Hausa/Fulani na Oyo da Kudancin Najeriya, yana mai rokon Allah ya jikansa da Rahama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: