An Tsallake Tinubu, Atiku An Ba Kwankwaso Lambar Karramawa a Najeriya

An Tsallake Tinubu, Atiku An Ba Kwankwaso Lambar Karramawa a Najeriya

  • Kungiyar Arewa Youth Democratic Movement ta karrama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin jagoran da ya fi bayar da gudunmawa a bana
  • Shugaban kungiyar, Muhammad Sabo Bakin Zuwo, ya ce tsohon gwamnan Kano ya cancanci wannan karramawa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa
  • Jama’a da dama sun nuna farin cikinsu da wannan lambar yabo, inda wasu suka bayyana shi a matsayin wanda zai zamo shugaban Najeriya na gaba a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wata Kungiya ta ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na daga cikin shahararrun jagororin siyasa a Najeriya da suka yi fice wajen tallafawa matasa da ci gaban al’umma.

Kungiyar matasan Arewa ta Democratic Movement ta karrama shi da lambar yabo ta jagoran da ya fi kafafa gwiwar jama'a.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Kwankwaso
An ba Kwankwaso lambar karramawa. Hoto: Hon Saifulahi Hassan
Asali: Facebook

Hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya wallafa yadda aka karrama shi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da bikin karramawar ne a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Muhammad Sabo Bakin Zuwo.

Kungiyar matasa ta karrama Kwankwaso

Shugaban kungiyar Arewa Youth Democratic Movement, Muhammad Sabo Bakin Zuwo, ya bayyana cewa an karrama Sanata Kwankwaso ne saboda irin gudunmawar da yake bayarwa.

Muhammad Sabo Bakin Zuwo ya bayyana cewa an karrama Kwankwaso ne saboda cigaba da yake kawowa wajen bunkasa rayuwar matasa.

Ya ce Kwankwaso jagora ne da ya taka rawar gani a fannoni da dama, musamman a bangaren ilimi, sana’o’i da ci gaban al’umma baki daya.

Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Martanin jama'a kan karramawar Kwankwaso

Bayan bayar da wannan lambar yabo, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan cancantar Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC a kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata

Wani mai suna Mohd Sidi ya rubuta cewa:

"Muna taya jagora murna. In sha Allahu, shugaban kasa ne na 2027."

Masoyan Kwankwaso sun yi farin ciki

Wasu daga cikin magoya bayan Kwankwaso sun masa addu'a wasu kuma sun masa fatan samun nasara a zabe mai zuwa.

Wani mai goyon bayan Kwankwaso, Shafiu Abdullahi ya ce:

"Duk wani abu da jagora ya karɓa, tabbas ya cancanta."

A daya bangaren, Sulaiman Sulaiman ya ce:

"Rabiu Musa Kwankwaso, shugaban kasa ne na gobe, in sha Allahu."

A nasa bangaren, Sani Yusuf ya yi addu’a da cewa:

"Allah ya kara rayuwa da albarka, jagoranmu."

Ana sa ran karramawar da aka yi wa madugun Kwankwasiyya za ta kara zaburar da shi kan cigaba da ayyukan da za su amfani jama'a, musamman matasa

Haka zalika an yi fatan kungiyar za ta cigaba da karrama shugabanni da ke bayar da gudunmawa wajen ci gaban matasa da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun taru sun ba shugaba Bola Tinubu mukamin sarauta mafi girma

An karya farashin abinci a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta hada kai da 'yan kasuwa domin karya farashin abinci a watan Ramadan mai albarka.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Kano ta karya farashin nau'ukan abinci har 17 da suka hada da shinkafa, masara, taliya da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng