GCON: Tinubu Ya Ba Sarkin Yarbawa Lambar Karramawa Ta 2 Mafi Girma a Najeriya

GCON: Tinubu Ya Ba Sarkin Yarbawa Lambar Karramawa Ta 2 Mafi Girma a Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya karrama Sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona da lambar girmamawa ta 'Grand Commander of Order of Nigeria'
  • Oba Sikiru wanda ya samu wannan lambar girmamawar ta GCON, ya kasance a kan karagar Sarkin Ijebu na tsawon shekara 64
  • Tinubu ya kuma taya basaraken murnar cika shekara 90 a duniya tare da bayyana shi a matsayin gwarzon dimokuradiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - A yau Juma'a ne shugaban kasa Bola Tinubu ya ba Awujale kuma babban sarkin kasar Ijebu, Oba Sikiru Adetona lambar girmamawa ta GCON.

An karrama Sarkin kasar Ijebu da lambar yabo ta GCON
Shugaba Tinubu ya karrama Sarkin Ijebu da da lambar girmamawa ta GCON. Hoto: Oba Sikiru Olukayade Adetona
Asali: UGC

An ba Oba Sikiru lambar yabo ta GCON

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an ba Oba Sikiru lambar yabo ta GCON ne saboda gudunmawar da ya bayar ga ci gaban kasa wadda ba za ta iya misaltuwa ba.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kuma ba da wannan lambar ne a wajen bikin cika shekaru 90 na basaraken, wanda aka gudanar a dakin taro na makarantar koyon mulki ta Oba Sikiru Adetona da ke a jami’ar Olabisi Onabanjo, jihar Ogun.

Tinubu ya gwarzanta Sarki Sikiru

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ne ya wakilci Tinubu a wajen taron kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Tinubu ya kuma umurci cibiyar nazari da koyon dabarun siyasa ta kasa da ke Kuru, Jos da ta karbi ragamar kula da makarantar mulki ta Oba Sikiru Adetona.

Shugaban ya bayyana Awujale a matsayin gwarzon dimokuradiyya da ake nunawa kauna saboda hikima da shawarwarin da yake bayarwa domin warware matsalolin kasar.

Sarkin Ijebu ya yi shekara 64 a mulki

An wallafa a shafin Wikipedia cewa an haifi Oba Sikiru Olukayade Adetọna a ranar 10 ga Mayu 1934, a cikin gidan sarauta na Anikinaiya na kasar Ijbu a garin Imupa, Ijebu Ode.

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: Ma'aikatar tsaro ta rabawa sojoji sababbin motocin yaki masu sulke

An nada shi a matsayin sarki a ranar 2 ga Afrilu 1960, wanda ya sa ya kasance daya daga cikin sarakuna mafi dadewa a kan karagar mulki a Najeriya.

A ranar 5 ga Afrilun 1960, sabon sarki Oba Adetọna ya hau kujerar sa a matsayin mamba na Majalisar Sarakunan Yamma, bayan amincewar gwamnan Yamma na wancan lokaci.

Buhari ya ba Tinubu lambar GCFR

A can baya, mun ruwaito maku cewa shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kasa na baya, ya ba Bola Tinubu lambar karramawa ta GCFR.

Buhari ya karrama Tinubu ne ana saura kwanaki huɗu kafin zuwan ƙarshen wa'adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu, yayin da ya ba Kashim Shettima lambar yabo ta GCON.

Asali: Legit.ng

Online view pixel