Jirgin shugaba Tinubu Ya Iso Najeriya Bayan Kwashe Makonni a Kasashen Waje

Jirgin shugaba Tinubu Ya Iso Najeriya Bayan Kwashe Makonni a Kasashen Waje

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan ziyarar da ya kai ƙasashen Netherlands da Saudiyya
  • Mai girma Tinubu ya dawo ne bayan ya shafe makonni biyu baya cikin ƙasar, kuma mako ɗaya bayan an yi masa gani na ƙarshe a Saudiyya
  • Dawowar shugaban ƙasan na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fito ya ƙalubalanci rashin sanin takamaiman inda yake

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ya shafe makonni biyu a ƙasashen waje.

Shafin NTA na manhajar X (wacce a baya aƙa fi sani da Twitter) ya ba da labarin dawowar shugaban ƙasar Najeriyan.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tafiyar Tinubu da aka ce ya 'ɓata' kafin ya dawo

Tinubu ya dawo Najeriya
Shugaba Tinubu ya dawo gida Najeriya daga kasashen waje Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tashar ta bayyana cewa shugaban ƙasan ya dawo gida Najeriya ne da safiyar ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka yi wa Tinubu ganin ƙarshe?

Lokaci na ƙarshe da aka ga Shugaba Tinubu shi ne a wajen taron tattalin arziƙi na duniya da aka gudanar a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

An dai gudanar da taron WEF ne a ranakun 28 da 29 na watan Afirilun 2024.

Tun da farko kafin jirginsa ya sauka a Saudiyya, Shugaba Tinubu ya ziyarci ƙasar Netherlands inda ya gana da Firaministan ƙasar.

Ina Tinubu ya shige daga tafiya ketare?

Bayan taron na Saudiyya, ƴan Najeriya da dama ba su san inda shugaban ƙasan yake ba, inda da dama daga ciki musamman ƴan adawa suka yi ta magana kan rashin zamansa a cikin ƙasar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan yadda aka bar Najeriya babu jagoranci alhalin ƙasar na fama da matsalolin tsaro da ke bukatar daukar matakai akai-akai.

Kara karanta wannan

Tinubu yana kasar waje saboda rashin lafiya? Minista ya fadi gaskiya

Yaushe Tinubu zai dawo Najeriya?

A wani labarin ne aka ji cewa fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinuɓu zai dawo gida Najeriya.

Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel