Shugaba Bola Tinubu ya Nemi Hadin Kan Kasashe Kan Matsalar da ta Addabi Duniya

Shugaba Bola Tinubu ya Nemi Hadin Kan Kasashe Kan Matsalar da ta Addabi Duniya

  • Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya nemi duniya ta hada hannu wajen kawar da matsalolin da su ka addabi duniya, ciki har da yunwa
  • Mai girma Bola Tinubu ya nemi hadin kan ne a taron duniya kan tattalin arziki da makamashi da ya gudana a birnin Riyadh da ke Saudiya
  • Ya ce bai kamata a dinga a barin nahiyar Afrika a baya ba kan batutuwan ci gaba musamman ta fuskar fasahar zamani da zuba hannun jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Riyadh, Saudiya - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi hadin kan duniya wajen yi wa matsalar yunwa taron dangi domin kawar da ita, da sauran matsalolin da su ka addabi al'umma.

Kara karanta wannan

"Abin da ya zama dole ne": Gaskiyar dalilin da ya sa Tinubu ya janye tallafin man fetur

Ya nemi hadin kan ne a taron duniya kan tattalin arziki da makamashi da ya gudana a birnin Riyadh da ke Saudiya.

Shugaban na ganin kamata ya yi duniya ta yi wa matsalar yunwa taron dangi
Shugaba Bola Tinubu ya mika bukatar hadin kan ne a taron duniya kan tattalin arziki Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya shaidawa taron shugabannin duniya cewa hadin kan, musamman da kasashen Afrika zai taimaka wajen gina rayuwa mai cike da walwala d ci gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yanzu lokaci ya yi da za a daina watsi da bukatar sanya hannun jari a nahiyar Afirka domin habaka tattalin arziki, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

"Afrika na da albarkatun kasa," Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa nahiyar Afrika na da yalwar tattalin arzikin kasa.

Ya ce samar da jari zai taimaka wajen bunkasa bangarorin noma, tattalin arziki, da kawar da yunwa.

Shugaban jaddada bukatar sanya nahiyar cikin batutuwan ci gaba ta fuskar fasaha, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana murna sauƙi ya fara samuwa, Tinubu ya sake tsoratar da 'yan Najeriya, ya yi jan ido

"Yan Najeriya na daf da jin dadi"

A baya an ji gwamnatin tarayya ta yi wa yan Najeriya alkawarin za su samu saukin rayuwa nan gaba kadan, tare da bayyana samar da sababbin shirye-shiryen tabbatar da kudirin gwamnatin.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shi ne ya bayar da tabbacin, inda ya ce gwamnatinsa ta shirya aiwatar da mafi karancin albashi domin kawo wa ma'aikata sauki.

Ya ce ba za a dauki wani lokaci mai tsawo ba abubuwa za su sauya zuwa na farin ciki a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel