Peter Obi Ya Yi Watsa Watsa da Gwamnatin Bola Tinubu Saboda Lafta Harajin 0.5% a Banki

Peter Obi Ya Yi Watsa Watsa da Gwamnatin Bola Tinubu Saboda Lafta Harajin 0.5% a Banki

  • 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour, Peter Obi ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan harajin tsaron yanar gizo
  • Peter Obi ya yi bayanin ne a safiyar yau Laraba, 8 ga watan Mayu cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafisa na X
  • 'Dan siyasar ya kuma yi kira na musamman ga gwamnatin kan abin da ya dace ta yi a halin da ake ciki na wahalar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

'Dan takarar Nigeria a zaben 2023 na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya caccaki kudurin gwamnatin tarayya na fara karban harajin tsaron yanar gizo.

Peter Obi
Peter Obi ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna rashin tausayi kan harajin 0.5%. Hoto: Peter Obi/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mista Peter Obi ya ce kudirin ba abin da zai haifar sai kara jefa 'yan Najeriya cikin sabuwar wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta shirin korar wadanda Ganduje ya dauka aiki

Ya yi martanin ne cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba, 8 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Peter Obi, harajin zai kara ruguza tattalin arzikin Najeriya da kuma kara nakasa 'yan kasa.

Peter Obi ya fadi abin da ya kamata ayi

Cikin sakonnin da ya rubuta ya ce a irin wannan lokacin da ake fama da wahalar rayuwa kokarin gwamanti na kirkiran haraji ya nuna cewa ba ta damu da halin da al'umma ke ciki ba.

Ya kara da cewa a halin da ake ciki kamata ya yi gwamantin Najeriya ta yi kokarin saukaka haraji ba karawa ba.

Obi: "Yadda harajin zai shafi kasuwanci"

Wurin tasiri a kan harkokin kasuwanci kuwa, cewa ya yi abin takaici shi ne harajin zai shafi uwar kudin masu hada-hada ne ba ribar da za su samu ba.

Kara karanta wannan

Kungiya ta maka gwamnoni 36 da minista Wike a kotu kan cin bashin N5.9tn da $4.6bn

Wanda hakan a cewarsa babbar barazana ce ga 'yan kasuwa da harkar kasuwanci a Najeriya baki daya.

Cikin shagube, Peter Obi ya ce a halin yanzu mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro ta zama mai karban haraji.

A karshe ya bayyana cewa kirkiro harajin abin takaici ne kuma ya kamata gwamnatin ta sake nazari a kai.

SERAP za ta kai Tinubu kotu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kare hakkin tattalin arziki (SERAP) ta yi barazanar kai shugaban kasa Bola Tinubu kotu a kan harajin tsaron yanar gizo.

Kungiyar ta bayyana cewa ta ba shugaban kasan sa'o'i 48 domin janye kalamansa kan kudurin harajin 0.5% ko kuma su hadu a gaban alkali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel