Kwanaki Kadan da Yin Juyin Mulki a Nijar, Bola Tinubu Ya Tafi Biki a Kasar Afrika

Kwanaki Kadan da Yin Juyin Mulki a Nijar, Bola Tinubu Ya Tafi Biki a Kasar Afrika

  • A yau Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar kwana guda zuwa Benin inda ake bikin samun ‘yancin-kai
  • Kwanaki hudu da hambarar da gwamnatin Nijar ne Shugaban Najeriyan zai bar Abuja zuwa Cotonou
  • Tawagar za ta kunshi hadimai da AdulRahmanAbdulRasaq, Nasir Idris da Mohammed Umar Bago

Abuja - A yau ne Bola Ahmed Tinubu zai amsa gayyatar da aka aiko masa, zai halarci bikin murnar kasar Benin na cika shekara 63 da ‘yancin kai.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin Dele Alake, an ji cewa a matsayinsa na shugaban Najeriya da ECOWAS, Bola Tinubu zai ziyarci Benin.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasar ya ce Mai girma Bola Tinubu zai zama babban bakon shugaba Patrice Talon a bikin da za ayi a yau.

Tinubu
Bola Tinubu da sauran Shugabannin Afrika Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu da Patrice Talon

Kara karanta wannan

Malaman Addinin Musulunci a Arewa Sun Roki a Hana El-Rufai Yin Minista, Sun Bayyana Dalili

Kafin ya yi shirin ziyartar kasar Afrikan, sai da shugaban Najeriya ya zauna da Patrice Talon a wajen taron da su ka halarta kwanaki a Faransa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga baya kuma su ka sake haduwa wajen taron kungiyar ECOWAS da aka yi a Guinea-Bissau, sannan sai su ka sa labule jiya a fadar Aso Rock.

The Nation ta ce Talon ya gayyaci takawaransa na Najeriya ya zo bikin taya su murnar samun ‘yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.

Dele Alake ya ce shugaba Tinubu ya ga bukatar inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta fuskokin kasuwanci, ciniki, al’adu da sauransu.

A sakamakon haka za a bunkasa yadda jami’an kwastam na kasashen za su kula da iyakoki.

'Yan rakiyar Bola Tinubu

Shugaban Najeriyan ya kira wasu gwamnoni shida da kuma mukarrabansa da za su yi masa rakiya zuwa wannan ziyara ta kwana guda da za a kai.

Kara karanta wannan

Mu je zuwa: Tinubu ya nada fitaccen masani don yin bincike a lamurran CBN

Gwamnonin nan su ne: Dapo Abiodun, Babajide Sanwo-Olu, Seyi Makinde, AbdulRahmanAbdulRasaq, Nasir Idris da kuma Umar Bago.

Jawabin Shugaba Bola Tinubu

A jawabin da aka yi jiya, labari ya zo mana Gwamnatin Bola Tinubu za ta batar da N100bn domin noma shinkafa da masara da shuka rogo da alkalama.

Nan da watanni, za a ga an raba motoci masu amfani da gas domin saukaka sufuri bayan tashin fetur, a yanzu Najeriya ta adana fiye da Naira tiriliyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel