Kwana 100 a Ofis: Jerin Kasashen Da Shugaba Tinubu Ya Ziyarta

Kwana 100 a Ofis: Jerin Kasashen Da Shugaba Tinubu Ya Ziyarta

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, ya cika kwana 100 a matsayin shugaban ƙasan Najeriya. An rantsar da shi ne a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tun daga lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasan Najeriya, Tinubu ya ziyarci aƙalla ƙasashe shida.

Jerin kasashen da Shugaba Tinubu ya ziyarta
Shugaba Tinubu ya ziyarci kasashe shida cikin kwana 100 a ofis Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ga jerin ƙasashen da shugaban ƙasar ya ziyarta a cikin kwana 100 da ya yi a ofis.

Tinubu ya halarci taro a Faransa

A matsayin shugaban ƙasan Najeriya, ƙasa ta farko da Tinubu ya fara zuwa ita ce Faransa, inda ya halarci wani taro kan tattalin arziƙi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tafiyar ta sa ta faru ne ƙasa da wata ɗaya bayan ya hau kan karagar mulkin shugabancin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu: Rabaran Mbaka Ya Gaya Wa Shugaba Tinubu Ya Shirya Barin Ofis? Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu ya gana da Buhari a Landan

Sati biyu bayan taron da aka gudanar a ƙasar Faransa, Shugaba Tinubu ya ziyarci birnin Landan, inda ya gana da magabacinsa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar 27 ga watan Yuni.

Ganawar ta su dai ita ce ta farko tun bayan da Buhari ya miƙa mulki a hannun Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Tinubu ya ziyarci Guinea Bissau

A ranar 9 ha watan Yuli, Shugaba Tinubu ya ziyarci ƙasar Guinea Bissau, inda ya halarci taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS.

A wajen taron, shugabannin ƙasashen sun zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ECOWAS.

Shugaba Tinubu ya shilla zuwa Kenya

A ranar Asabar, 15 ga watan Yuli, ƙasar Kenya ta zama ƙasar Afirika ta biyu wacce Shugaba Tinubu ya ziyarta a cikin kwanakinsa 100 na farko da ya yi a ofis.

Tinubu ziyarci ƙasar Benin

Kara karanta wannan

Manya-manyan Bukatu 5 Da Peter Obi Ya Mikawa Kotu Kan Shari'arsa Da Bola Tinubu

A ranar Talata, 1 ga watan Agustan 2023, Shugaba Tinubu ya ziyarci ƙasar Benin tare da gwamnoni shida domin bikin zagayowar ranar samun ƴancin kasar daga Faransa.

Shugaban ƙasar ya yi tafiyar ne a lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta sanar da fara zanga-zanga domin nuna adawa da cire tallafin man fetur wanda ya jawo tsadar rayuwa a ƙasa.

Tinubu ya shilla zuwa birnin New Delhi, India

A ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, lokacin da ya cika kwana 99 a ofis, shugaban ƙasa Tinubu ya shilla zuwa birnin New Delhi, babban birnin ƙasar India, domin taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar G20.

Shugaba Tinubu ya halarci taron ne bisa gayyata ta musamman da Firaministan India, Narendra Modi ya aike masa.

Gaskiyar Abin Da Mbaka Ya Ce Kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi ta yaɗa wasu maganganu masu cewa Rabaran Mbaka ya ce Shugaba Tinubu ya shirya barin ofis.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Ministoci 2 Da Manyan Hafsoshin Tsaro Kan Muhimmin Abu

Sai dai, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa an sauya kalaman babban faston ne, domin ba abin da ya ce ba kenan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel