Harajin CBN: Na Hannun Daman Tinubu Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi

Harajin CBN: Na Hannun Daman Tinubu Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi

  • Yayin da Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo sabon tsarin biyan haraji, Daniel Bwala ya yi martani kan lamarin
  • Tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce ya kamata 'yan Najeriya su sake jikinsu domin rungumar tsarin
  • Lauyan ya bayyana haka ne a yau Laraba 8 ga watan Mayu inda ya ce Tinubu ya na matukar jin tausayin 'yan kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Daniel Bwala, tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba 'yan Najeriya shawara.

Bwala ya bukaci 'yan ƙasar suyi gaggawar sabawa da tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu musamman kan harajin tsaron yanar gizo.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi watsa watsa da Gwamnatin Bola Tinubu saboda lafta harajin 0.5% a banki

Bwala ya ba 'yan kasa shawara kan sabon tsarin CBN da Tinubu ya kawo
Daniel Bwala ya ce dole 'yan Najeriya su rungumi tsarin harajin CBN da Bola Tinubu ya kawo. Hoto: @BwalaDaniel, @officialABAT.
Asali: Twitter

Abin da Bwala ya fada kan Tinubu

Lauyan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Laraba 8 ga watan Mayu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya musanta cewa Tinubu bai kula da halin da ake ciki inda ya ce wahala ba za ta tabbata ba.

Tsohon hadimin Atiku na magana ne kan sabon tsarin harajin 0.5% da bankin CBN ya kawo domin tsaron yanar gizo.

Za a shiga wahala a mulkin Tinubu

"Babu wanda ya ke tunani cewa shugaban kasa ya dauki wannan mataki wanda ya zama dole ba za a sha wahala na wani dan lokaci ba."
"Kamar lokaci ne na haihuwa dole za a sha wahala kadan kuma dole za a sadaukar."
"Idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan hali abin da ya kamata ya yi shi ne kokarin sabawa da hakan, wahala ba za ta ɗore ba, wannan shi ne tsarin rayuwa."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa ya bukaci shugabanni su yi koyi da marigayi Yar'adua

- Daniel Bwala

Bwala ya ce Tinubu ya sha fada cewa 'yan Najeriya suna cikin wani hali wanda ya fadi hakan ya fi a kirga.

CBN ya ƙaƙaba sabon harajin 0.5%

Kun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo sabon tsarin biyan haraji domin tsaron yanar gizo a kasar baki daya.

Bankin daga bisani ya jero wasu hada-hadar kudi 16 da wannan sabon tsarin biyan haraji ba zai shafa ba a kasar.

'Yan ƙasar da dama sun kushe sabon tsarin da babban bankin ya kawo inda suka koka kan halin da a yanzu 'yan Najeriya ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel