Shugaba Tinubu Ya Gana da Buhari a Birnin Landan, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Gana da Buhari a Birnin Landan, Bayanai Sun Fito

  • Kafin dawowa gida Najeriya, Shugaba Tinubu ya gana da magabacinsa, Muhammadu Buhari a Landan na kasar Burtaniya
  • Har yanzu babu cikakken bayani kan abinda manyan jiga-jigan biyu suka tattauna amma Hoton ganawarsu ya karaɗe soshiyal midiya
  • Tun ranar 20 ga watan Yuni shugaba Tinubu ya nufi kasar Faransa domin halartar taro, daga bisani kuma ya wuce Landan

Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban kasan da ya gabace shi, Muhammadu Buhari, a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa har yanzu ba bu wanda ya san sakamakon zaman manyan jiga-jigan biyu saboda har kawo yanzu ba'a fitar da sanarwa kan abinda suka tattauna ba.

Hoton ganawar Tinubu da Buhari a Landan.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Tinubu a Birnin Landan, Bayanai Sun Fito Hoto: APC Newspaper
Asali: Facebook

Sai dai a halin yanzu wasu daga cikin hadiman shugaban kasa sun wallafa Hotunan taron a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Kalubale Mafi Tsanani Da Ya Fuskanta A Rayuwa

Idan baku manta ba shugaba Tinubu ya bar Najeriya a ranar 20 ga watan Yuni, 2023 domin halartar taron kwana biyu kan kuɗi wanda ya gudana a birnin Farisa na ƙasar Faransa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan ne karo na farko da shugaban ya yi tafiya a hukumance tun bayan da ya karɓi ragamar mulkin Najeriya daga hannun Buhari ranar Litinin 29 ga watan Yuni, 2023.

Tun da fari, shugaban ƙasan ya tsara dawowa gida Najeriya ranar Asabar 24 ga watan Yuni, 2023 amma ya yanke zarce wa zuwa birnin Landan na ƙasar Burtaniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Dele Adeleke, ya fitar ya ce Bola Tinubu zai biya birnin Landan a wata ziyara ta kai da kai.

Amma a cewarsa, shugaban zai dawo gida ya yi babbar sallah (Eid-el-Kabir) a mahaifarsa jihar Legas.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jirgin NAF Ya Yi Luguden Wuta Kan Mafakar 'Yan Ta'adda 3 a Arewa, Rayuka Sun Salwanta

Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki a Kasashen Waje

A wani rahoton na daban kuma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan halartar taron kudi a kasar Faransa da kuma ziyarar da ya kai Landan.

Tinubu ya sauka a sashin shugaban kasa na filin jirgin Murtala Muhammed a jihar Legas da misalin karfe 5:05 na yammacin yau Talata, 26 ga watan Yuni, 2023.

Ya samu tarba daga tawagar magoya bayansa waɗanda suka jima a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa tsawon awanni suna dakon isowarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel