An Cire Takunkumi: Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Daga Zama da Shugaban UAE

An Cire Takunkumi: Tinubu Ya Cin Ma Nasarori 3 Daga Zama da Shugaban UAE

  • Babu maganar a hana jirgi tashi daga Najeriya zuwa kasar UAE ko makamancin haka
  • Alherin zaman da Bola Tinubu ya yi da shugaba Mohamed bin Zayed Al Nahyan ta fito fili
  • Gwamnatin Najeriya ta sasanta da UAE, har an cin ma yarjejeniyar canjin kudin ketare

Abuja - Sanarwa ta fito yanzu nan daga fadar shugaban kasar cewa an kawo karshen takunkumin da aka kakabawa ‘yan Najeriya zuwa UAE.

A yau Litinin, Mai girma Bola Ahmed Tinubu da shugaban UAE, Mohamed bin Zayed Al Nahyan su ka cin ma matsaya a zaman da su ka yi.

Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale ya fitar da wannan sanarwa a shafin Facebook.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a UAE Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Za a cigaba da bada bizar UAE

Da rana tsaka Mohamed bin Zayed Al Nahyan ya zauna da Bola Tinubu a Abu Dhabi domin karkare magana a kan takunkumin takardar biza.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Tayi Karin Haske a Kan ‘Shirye-Shiryen’ Kirkiro Sababbin Haraji

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kafin yanzu UAE ta hanamutanen Najeriya shiga kasarta, amma daga yanzu za a cigaba da bada takardar biza ga duk wanda yake bukata.

Wata nasara da aka cin ma a ranar nan mai tarihi ita ce kyale jiragen kamfanonin Etihad da Emirates su cigaba da zuwa UAE daga Najeriya.

Nawa Najeriya ta biya kasar UAE?

Ngulale ya ce sansantawar da aka yi ba ta nufin gwamnatin Najeriya ta biya kobo ga takwararta.

Tinubu ya nuna akwai bukatar hadin-kai tsakanin kasarsa da ta larabawan, ya kuma amince da yarjejeniyar da aka cin ma a zaman na Litinin.

Dawo da kyakkyawar alaka za ta yi sanadiyyar cin moriyar miliyoyin dalolilin kudi a shekara.

Sanarwar Ajuri Ngelale ta ce Kasar UAE da Najeriya su na amfana da juna ta fuskokin tsaro, harkar gano da kuma cinikin makamai.

Kara karanta wannan

Jajirtaccen Shugaba: Yadda Shugaban Kasar Amurka ya Jinjinawa Mulkin Tinubu a Indiya

Tinubu ya yabawa Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya ce nan gaba kadan za a sanar da sabon yarjejeniyar canjin kudi da kasar wajen.

Tinubu zai saukaka biyan haraji

Fadar shugaban kasa ta ce ‘Yan Najeriya su daina tunanin karin haraji da yawan canjin dokokin kudi, an fahimci babu niyyar lafto wasu haraji

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce aikinta shi ne rage adadin masu biyan haraji, rahoto ya zo dazu cewa za ragewa marasa karfi nauyin da ke wuyansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel