Kasashen duniya za su bada tallafin $2.53bn don yaki da ta'addancin Boko Haram

Kasashen duniya za su bada tallafin $2.53bn don yaki da ta'addancin Boko Haram

- A ci gaba da taron kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Berlin, sakamakon taron zai samar da tallafin $2.53bn don yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi

- Taron wanda ya samu halartar sama da kasashe 70 na duniya, ya kuma samu halartar kungiyoyin kasa da kasa dama kungiyoyi masu zaman kansu

- Ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje ta kasar Jamus, ta ce za'a raba kudaden ne "a shekaru masu zuwa" ga Nigeria, Chadi, Niger da Kamaru

Babban taron kasa da kasa don bada tallafi kan yadda za'a kawo karshen kungiyar yan ta'adda ta Boko Haram, da ke gudana a kasar Berlin, ya yi alkawarin samar da zunzurutun kudi dala Biliyan biyu da Miliyan hamsin da biyu, don tallafawa kasashen da ke yankin tafkin Chadi wajen yaki da Boko Haram.

Ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje ta kasar Jamus, ta ce za'a raba kudaden ne "a shekaru masu zuwa" ga Nigeria, Chadi, Niger da Kamaru, inda aka fi samun yawan kai hare haren mayakan na Boko Haram, wadanda ke da manyan sansanoninsu a tafkin Chadi.

Taron wanda za'a gudanar a cikin kwanaki biyu, wanda ya samu halartar sama da kasashe 70 na duniya, manyan kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, sun tara $672m a shekara ta 2017.

Mr. Mark Lowcock, sakarare kan harkokin bada tallafi da gudanar da ayyukan kai daukin gaggawa a Majalisar Dinkin Duniya, ya godewa masu bada tallafin, bisa wannan babban yunkuri nasu.

KARANTA WANNAN: Nayi nadamar gudunmawar miliyoyin da na bawa APC a 2014 – Ekweremadu

Lowcock ya ce:"Wannan tallafi da kuka bayar a taron yadda za'a kawo karshen ta'addanci a yankin tafkin Chadi zai taimaka wajen ceto rayukan al'ummar da ke zaune a ciki da wajen yankunan tafkin."

Kamfanin dillancin labarai na NAN, ya tattara bayani kan yadda tallafin ya kasance, in kasar Jamus, wacce ta gabatar da taron, ta bada Euro Miliyan 265, yayin da kasar Norway ta bada $125m.

Sauran kasashen sun hada da Amurka, wacce ta bada $420m; Switzerland, $20m; Faransa, Euro Miliyan 131; Belgium, Euro Miliyan 45; Finland, Euro Miliyan 2.3; da kuma Denmark, $72.5m.

NAN ta ruwaito cewa kasar Burtaniya ta bada tallafin Fam Miliyan 146; Canada, CAD, $68m; Hadakar kungiyar kasashen turai, Euro miliyan 231.5; Luxembourg – Euro miliyan 40; yayin da kasar Sfaniya ta bada Euro miliyan 3.2.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng