Tinubu Ya Fadi Abu 1 da Za a Yi Wa Masu Neman Cin Hanci a Gwamnatinsa

Tinubu Ya Fadi Abu 1 da Za a Yi Wa Masu Neman Cin Hanci a Gwamnatinsa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa da kuma ƙudurinsa na yin aiki da masu zuba jari ƴan ƙasar Qatar
  • Tinubu ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai wajen taron kasuwanci da zuba jari na Najeriya da Qatar a Doha, babban birnin ƙasar
  • Shugaba Tinubu ya yi wani kwakkwaran bayani a wurin taron inda ya ƙarfafa gwiwar masu zuba jari daga ƙasashen waje su kai rahoton duk wani jami’insa da ya nemi na goro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Doha, Qatar - Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya buƙaci masu zuba hannun jari da su fallasa jami’an Najeriya da ke neman cin hanci.

Ya kuma bai wa masu zuba jari ƴan ƙasar Qatar tabbacin cewa Najeriya a shirye take domin yin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Dattawa sun tsoma baki kan batun sojoji su kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu kan abu 2

Shugaba Tinubu ya je Qatar
Tinubu ya halarci taro mai muhimmanci a Qatar Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Ajuri Ngelale, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce:

"Na zo nan ne domin in ba ku tabbacin cewa gyare-gyare na gudana, ku manta da duk abin da ku ka ji a baya.
"Kowane irin cikas ko matsala da wasunku za su fuskanta a baya ne, domin babu wani cikas a nan gaba."

Tinubu ya ja hankalin masu zuba jari na Qatar

Tinubu ya kuma tabbatar wa masu zuba jari daga ƙasar Larabawan cewa jarin da suke zubawa zai kasance mai ƙima da amfani.

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa:

“Kada ku bayar da cin hanci ga kowa daga cikin mutanenmu, kuma idan an nema ko an karɓa, ku kawo mana rahoto. Za ku samu damar zuwa gare ni.

Kara karanta wannan

"Mu ba ƴan siyasa bane" Ƴan ƙwadago sun maida zazzafan martani kan kalaman Shugaba Tinubu

"Ba za a sake ɗaukar matsayin Najeriya kan abin da ya gabata ba, sai dai da abin da muke yi a yanzu da kuma gaba.
"Kada ku bari gutsiri tsoma ya zama cikas ga nufin ku na saka hannun jari. Najeriya da gaske take game da kawo sauyi kan inganta zuba jari. Muna kawar da duk wani ƙalubale a yau kuma za mu ci gaba da yin hakan.
"Mun yi abubuwa da yawa a cikin watanni tara. Kuma ina tabbatar muku, za ku iya shiga ku fita duk lokacin da kuke so. Kuɗaɗen ku ba za su samu matsala ba wajen shiga da fita ƙasarmu. Ku zo ku zuba hannun jarin ku."

Umahi Ya Goyi Bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan ayyuka, David Nweze Umahi, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas, ba za su yi zanga-zanga ba don adawa da Tinubu.

Ministan wanda tsohon gwamnan jihar Ebonyi ne, ya yi nuni da Shugaba Tonubi ya yi wa mutanen yankin ayyukan da suka dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel