Rayuwa Za Ta Yi Sauki Kuma Abinci Zai Wadata a Mulkina, Tinubu Ya Dauki Alkawari

Rayuwa Za Ta Yi Sauki Kuma Abinci Zai Wadata a Mulkina, Tinubu Ya Dauki Alkawari

  • A yayin kaddamar da fara aikin titin Bida zuwa Minna a jihar Neja, Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin wadatar da ’yan najeriya da abinci
  • Shugaba Tinubu wanda ya samun wakilcin ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce zai tabbatar abinci ya wadata a wa'adin mulkinsa
  • Mun ji ta bakin 'yan Najeriya kan wannan alkawari na shugaban kasar, sai dai da alama, akwai jan aiki a gaban Tinubu kafin gamsar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Neja - Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta dogara da kanta wajen samar da abinci a yayin da yake kan mulki.

Shugaban kasar ya kuma tabbatar da cewa zai goyi bayan duk wani kokari na bunkasa jihar Neja, inda aka karrama shi da sarautar gargajiya ta Jagaban Borgu shekaru 20 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya, ya dakakar da tsarin biyan harajin 0.5% da CBN ya kawo

Bola Tinubu ya yi magana kan wadatar da abinci a Najeriya
Tinubu ya sha alwashin samar da isasshen abinci kafin karewar wa'adin mulkinsa. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya kaddamar da ginin titi

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin da yake kaddamar da fara aikin titin Bida zuwa Minna mai nisan kilomita 84, jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma ruwaito cewa, titin wanda aka kaddamar da fara gininsa a garin Kakakpagi, karamar hukumar Katch, zai lakume Naira biliyan 169.7.

Jaridar Tribune ta ruwaito shugaban kasar ya kuma yi kira ga sauran shugabannin jihohi da su yi koyi da irin wannan namijin kokari na gwamnan Neja, Mohammed Bago.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen taron kuma ya ba da tabbaci na hadin guiwa.

Tinubu zai sa abinci ya wadaci Najeriya

Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki kafada-da-kafada da jihohi domin samar da isasshen abinci a wannan wa'adin mulkinsa, in ji rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

"Gwamnatin tarayya za ta tallafawa jihar Neja da sauran jihohi domin samar da ci gaba mai dorewa wanda dole yana bukatar hadin guiwa daga matakan gwamnati."
"Zan tabbatar da ganin cewa Najeriya ta samu wadaccen abinci a karkashin mulkina. Za mu gina tituna masu kyau domin kare rayuka da kuma bude kofofin bunkasar tattali arziki."

- Bola Tinubu

'Yan Najeriya sun yi martani kan alkawarin

Lagos-Kano: Za a kaddamar da layin dogo

A wani labarin, mun ruwaito maku gwamnatin tarayya ta ce a watan Yunin 2024 za ta kaddamar da fara jigilar kayayyaki a kan layin dogo da ya taso daga Lagos zuwa Kano.

Ministan sufuri, Saidu Alkali wanda ya bayyana hakan, ya ce layin dogon zai tsawaita karkon manyan titunan Najeriya tare da rage yawan mutanen da ke mutuwa a hatsarin mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel