Dangote, Dantata da Jerin Kanawa 8 da ke cikin Sahun Masu kudin Najeriya

Dangote, Dantata da Jerin Kanawa 8 da ke cikin Sahun Masu kudin Najeriya

  • Kusan kowa ya san Kano tsohon gari ne da ya shahara da harkar kasuwanci a Duniya tun fil azal
  • Ba abin mamaki ba ne a samu manyan masu kudin Najeriya sun fito daga wannan yanki na kasar nan
  • Kasar Kano ce ta fitar da Alhassan Dantata, wanda zuri’arsa har yau ta ke cikin sahun farko a dukiya

Kano - A rahoton nan da NewsWire ta fitar, an tattaro shahararrun masu kudin da ake da su daga jihar Kano. Ba Legit.ng ce ta gudanar da wannan bincike ba.

Kamar yadda aka yi bayani, jerin ya kunshi sanannun mutane ne, don haka akwai dinbin Attajiran da ba a ambaci sunayensu ba domin ba su shahara sosai ba.

Ga jerin nan kamar haka:

1. Alhaji Aliko Dangote

Ba a Kano ba, duk idan za a yi maganar masu kudin Afrika, dole a ambaci Alhaji Aliko Dangote. Shugaban kamfanin na Dangote Group ya mallaki Dala biliyan 13 a yau.

Kara karanta wannan

Iree: An Samu Wasu ‘Yan Iskan Gari Sun Je Fadar Sarki, Sun Banka Masa Wuta

2. Abdulsamad Rabiu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abdulsamad Rabiu shi ne mutum na biyu a jerin Attajiran Kano, maganar da ake yi, yana da Dala biliyan 3.2. Shugaban kamfanin na BUA, mutum ne mai son yin kyauta.

3. Rabiu Musa Kwankwaso

Jaridar ta kawo Rabiu Kwankwaso a Attajiran da ake da su a Kano, ana zargin yana da $950m. Mahaifinsa Basarake ne, amma shi babban ‘dan siyasa ne kuma manomi.

4. Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi II yana cikin wannan jerin, ana zaton dukiyarsa ta kai $480m. Sanusi II Attajirin Basarake ne, ‘dan kasuwa, masanin aikin banki.

5. Abdullahi Umar Ganduje

Kafin zamansa Mataimakin Gwamna da Gwamna, Abdullahi Ganduje ya rike Kwamishina sau da-dama, ya kuma yi aiki a Abuja, ana lissafin yana da $400m.

Manyan Kano
Muhammad Sanusi II MFR, Aliko Dangote, GCON, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u CON. Hoto: @baba
Asali: Twitter

6. Ibrahim Shekarau

Wani ‘dan siyasa daga Kano da ke cikin rukunin masu kudi shi ne Ibrahim Shekarau. Rahoton ya ce tsohon malamin makarantar ya shiga kasuwa, yanzu ya na da $150m.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun kama wasu kudade N19.5 a hannun abokan 'yan bindiga 5 a Arewa

7. Ghali Umar Na’Abba

Har wa yau mu na da tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Ghali Umar Na Abba wanda ya gaji kamfanin mahaifinsa a 1980s, tun lokacin ya samu makudan kudi.

8. Auwalu Abdullahi Rano

Alhaji Auwalu Abdullahi Rano shi ne shugaban kamfanin A.A. Rano Nigeria Ltd. A wani kaulin, ana maganar yana da kusan Dala biliyan 2, ya yi kudi ne da harkar mai.

9. Basheer Mohammed Garba

Basheer Mohammed Garba wanda aka fi sani da Lado, Attajiri ne kuma ‘dan siyasa. Lado ya samu kudi ta harkar kasuwanci, banki, da siyasa, yana cikin Attajiran Kano.

10. Bello Hayatu Gwarzo

Sai da Bello Hayatu Gwarzo ya yi shekara 16 a matsayin Sanata a Majalisa. Sanata Gwarzo ya tashi ne a gidan manya, yanzu ana lissafin ya ba Dala miliyan 20 baya.

Akwai wasu da ba ambace su ba a wannan rahoto irinsu Aminu Sule Garo, Bashir Yusuf Ibrahim, Ahmed Idris, Shamsuddeen Usman, da Abubakar Bashir Maishadda.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Najeriya na cikin matsala

An samu labar cewa tsakanin 1 ga watan Junairu zuwa 30 ga watan Afrili, an kashe Naira Tiriliyan 4.72 a Najeriya, amma 40% na kudin duk sun tafi wajen biyan bashi.

Abin da Gwamnatin Tarayya ta tatsa bai wuce Naira Tiriliyan 1.6, Ministar kudi ta kas ta ce bashin da aka biya ya zarce abin da aka iya samu da Naira Biliyan 300.

Asali: Legit.ng

Online view pixel