Aminu Daurawa: Shawarwari 5 Da Na Ba Ummita Kafin Mutumin China Ya Kasheta

Aminu Daurawa: Shawarwari 5 Da Na Ba Ummita Kafin Mutumin China Ya Kasheta

  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana tattaunawar da suka yi da Ummakulsum Buhari kafin a kashe ta
  • Shehin malamin yace ya ba Marigayiyar shawarwari a game da shirinta na auren Mista Gheng Quanrong
  • Jim kadan bayan haka sai aka ji labari cewa wannan mutumin kasar Sin ya hallaka masoyiyarsa

Kano - Shehin malamin nan Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayanin wayar da yayi da Marigayiya Ummakulsum Buhari wanda wani ‘dan kasar Sin ya kashe.

Daily Nigerian ta kawo rahoto cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yace a makon jiya, Ummakulsum Buhari tayi masa bayanin halin da take ciki da gidansu.

Babban malamin yake cewa wannan Baiwar Allah da aka sani da Ummita ta fada masa cewa iyayenta sun hana ta auren wannan saurayi da ya zo daga Sin.

Legit.ng Hausa ta fahimci Shehin ya yi wannan bayani a karshen darasinsa na karatun tarihin Annabi Muhammad (SAW) na Arrahiqil Makhutum a ranar Lahadi.

Sai an yi taka-tsan-tsan da irin wannan

Aminu Daurawa yace ya ba iyayen gaskiya, ya kuma fadawa Ummakulsum Buhari wasu shawarwari da ya kamata ta dauka kafin ta auri wannan bakon mutum.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bidiyon da aka wallafa a Facebook, malamin ya yi bayanin hadarin auren mutum ba tare da an yi bincike ba, domin zai iya tserewa ya bar mace da 'yan yara.

Ummakulsum Buhari
Ummakulsum Buhari Hoto saharareporters.com
Asali: UGC

Shawarwarin Sheikh Aminu Daurawa

Da farko Sheikh Daurawa yace dole a tuntubi hukumar shige da fice, domin a tabbatar da abin da ya kawo wannan mutumi Najeriya, sannan kuma a ji sana’arsa.

Shehin ya fadawa Marigayiyar cewa Sarkin Kano ya nada Sarkin Sinawa mazauna garin, don haka sai a nemi Sarkinsu domin bada shaida a kan masoyin na ta.

Baya ga haka, Daurawa yace ya kamata a sanar da ofishin jakadancin kasar Sin a game da wannan Basine da ke neman auren ‘Yar Kano domin hukuma ta sani.

'Dan kasar Sin ya musulunta

Bugu da kari, tsohon shugaban na Hisbah ya bada shawarar a hada da hukumar a cikin maganar domin su koyawa wannan mutumi addini tun da ya musulunta.

Da zarar an cika wadannan sharuda, malamin yace shi zai shiga gaba domin gamsar da iyayen Ummita ta auri ‘Dan kasar Sin, tun da bai sabawa musulunci ba.

Aminu Daurawa ya yi wa marigayiyar addu’a, ya kuma yi kira ga jama'a da hukumomin Najeriya su sa ido wajen kula da mutanen waje da ke shigowa.

Abin da ya sa na kashe ta - Quanrong

A ranar Lahadi ne aka ji labari Geng Quangrong ya bayyana cewa ya sokawa budurwarsa, Ummu Kulthum, wuƙa har lahira ne saboda ta ci amanarsa.

A halin 'yanzu yan sanda na cigaba da bincike kan labarin. Tuni dai jama'a su ka shiga kira ga hukuma a yankewa wa wannan mutumi hukuncin da ya dace

Asali: Legit.ng

Online view pixel