Dalilin Da Yasa Na Kashe Budurwata UmmuKulthum a Kano, Dan Chana Ya Magantu

Dalilin Da Yasa Na Kashe Budurwata UmmuKulthum a Kano, Dan Chana Ya Magantu

  • Geng Quangrong, ɗan asalin ƙasar China mazaunin Kano da ya kashe wata budurwa ya magantu kan dalilin aikata kisan
  • A ranar Jumu'a, Deng, wanda bayanai suka nuna suna soyayya da Mamaciyar, ya kutsa har gida ya daɓa mata wuƙa har lahira
  • A halin yanzun yan sanda na cigaba da bincike kan Kes din yayin da mutane ke ta kiraye-kirayen a mata adalci

Kano - Mutumin nan ɗan China mazaunin jihar Kano, Geng Quangrong, ya bayyana cewa ya soka wa budurwarsa, Ummu Kulthum, wuƙa har lahira ne saboda ta ci amanarsa.

Idan baku manta ba, ɗan China ya je har gidansu budurwar dake Anguwar Kabuga, Ɗorayi Babba, ya kasheta ranar Jumu'a da ta gabata, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Dan China da ya kashe budurwa a Kano.
Dalilin Da Yasa Na Kashe Budurwata UmmuKulthum a Kano, Dan Chana Ya Magantu Hoto: pmnews
Asali: Twitter

Deng ya amsa laifinsa na aikata kisan kai bayan dakarun 'yan sanda sun kama shi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

A cewar mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen Kano, Abdullahi Kuyawa, wanda ake zargi ɗan shekara 47, ya aikata wannan ɗanyen aikin ne bayan ya kutsa gidansu mamaciyar, inda ya rinƙa soka mata wuka har rai ya yi halinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa ya kashe budurwar?

Geng ya yi zargin cewa Ummu ta masa alƙawarin zata aure shi amma daga baya ta saɓa alƙawarin bayan ya kashe maƙudan kuɗi a kanta.

A jawabin da ya yi wa yan sanda, Ɗan China ya bayyana cewa saɓa alƙawarin ya fusata shi sosai, bisa haka zuciyarsa ta raya masa ya je har gida ya kasheta.

Kiyawa ya ƙara da cewa Mahaifiyar yarinyar ce ta rinka kururuwar neman taimako lokacin da Deng ke aikata ɗanyen aikin kuma nan take aka sanar da yan sanda suka kai ɗauki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Tuni dai kwamishinan yan sanda ya umarci DPO na Caji Ofis ɗin Ɗorayi Babba ya kula da lamarin, inji Kakakin yan sandan Kano.

Wane hali ake ciki game da Kes ɗin?

Legit.ng ta fahimci cewa a halin yanzun an maida ɗan Chinan sashin binciken mayan laifuka na Hedkwatar yan sanda dake Bampai, Kano domin tsananta bincike da kuma miƙa shi Kotu.

A ɗaya ɓangaren kuma, tuni aka Sallaci marigayya Ummu Kulthum aka kaita makwancinta ranar Asabar da Safe yayin da yan uwa da abokanan Arziki ke jimamin rasuwarta ba zato.

A wani labarin kuma mun kawo muku Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Bidiyon Marigayiya Ummita da kawarta sarauniya ya bayyana a shafukan soshiyal midiya inda suke hira kan mutuwa.

Wannan hirar tasu ta taba zukatan jama'a da dama musamman yadda marigayiyar ta nuna tawali'u a zantukarta, tana mai cewa kowa da tasa kaddarar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

Asali: Legit.ng

Online view pixel