Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da 'Bam' Ya Fashe A Jalingo

Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da 'Bam' Ya Fashe A Jalingo

  • Wani abun fashewa da ake tsammanin Bam ne ya tashi a kusa da wata mashaya a Jalingo, babban birnin jihar Taraba
  • Bayanai sun nuna cewa mutane sun shiga fargabar rashin sanin abinda zai faru nan gaba bayan aukuwar lamarin ranar Lahadi da daddare
  • Wannan shi ne karo na huɗu da irin haka ta faru a birnin Jalingo bayan shigowar wannan shekarar

Taraba - Mutane sun shiga yanayi na tashin hankali ranar Lahadi bayan wani abun fashe wa da ake kyautata zaton Bam ne ya tashi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Channels TV ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:35 na dare a wani wuri dake kusa da Shataletalen farko a Titin da zai kai ka Jami'ar jihar Taraba.

Wasu wurare da Bam ya taɓa a Jalingo.
Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da 'Bam' Ya Fashe A Jalingo Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Tashin Bam ɗin ya taba gine-ginen shaguna da wasu gidajen mutane a yankin.

Kara karanta wannan

Fasto da mabiyansa sun sha bulala yayin da wasu tsageru suka farmaki coci a jihar Arewa

Ganau sun yi ikirarin cewa an dasa Bam ɗin a bayan wata mashaya da mutane ka tattaruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wata ƙaramar yarinya da bata wuce shekara hudu ba na kwance tana bacci a Shagon lokacin da ginin ya rufta," inji wani mazauni da ya nemi a sakaya bayanansa.

Ya ƙara da cewa, "bisa sa'a ta tsira kuma a halin yanzun tana kwance ana kula da lafiyarta a Asbiti."

Duk da cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar fashewar amma yan sanda sun mamaye yankin domin daƙile tashin wani Bam ɗin idan mai yuwuwa an dasa wani a kusa.

Mazauna Anguwar da lamarin ya faru sun nuna fargabarsu kan abinda ka iya zuwa ya dawo nan gaba, inda suka ce wannan fashewar ita ce ta hudu a jerin tashin 'Bam' da ya addabi jihar tun farkon shekarar nan.

Kara karanta wannan

Abinda Ya Sa Har Yanzu Bamu Magance Ayyukan Ta'addanci Ta Layukan Waya da NIN Ba, Pantami Ya Magantu

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya tabbatar da lamarin ga jaridar The Cable da safiyar Litinin. Yace babu wanda ya jikkata sanadin tashin Bam ɗin.

Yace dakarun kwance Bam na hukumar 'yan sanda sun zagaye yankin kuma tuni aka fara bincike don gano musabbabin da ya jawo fashewar.

"Ba'a rasa rai ba, babu wanda ya ji rauni. Wani abu ne ya fashe da daren jiya, an tura masu ilimin kwance Bam, a halin yanzu muna jiran sakamako ne," inji shi.

Wani mazaunin Jalingo, Ishaq Na'ahwai, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa tabbas sun ji karar fashewa jiya da daddare a ATC Gress Junior Bye Pass.

"Tabbas mun ji fashewan abu jiya da dare, da na yi bincike kuma nasamu labari cewa tukunyan Gas ce don akwai aboki na da suke zama a wurin sun ce Gas ne domin sun gani da idonsu," Inji Ishaq.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Babban Hadimin Gwamnan Arewa, Sun Yi Ɓarna

Ya ƙara da cewa "Babu wanda ya mutu ko rauni, hasalima wata mata ke girki kuma ta bar wajen, bata kusa lokacin da ya fashe."

A wani labarin kuma kun ji cewa An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

Yan sanda sun ce sun kama wani babban ɗan bindiga da ya addabi mutane, Umar Namaro, a jihar Zamfara.

Muhammed Shehu, kakakin yan sandan jihar yace dakaru sun kama wani Sojan Bogi ɗauke da muggan makamai a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel