Kungiyar ’Yan China a Najeriya Ta Yi Allah Wadai da Kisan Ummita

Kungiyar ’Yan China a Najeriya Ta Yi Allah Wadai da Kisan Ummita

  • Kungiyar 'yan China mazauna jihar Kano sun bayyana bacin rai da jimamin mutuwar matashiya Ummita
  • A makon da ya gabata ne wani dan China ya shiga har gida ya caccakawa budurwarsa 'yan Najeriya wuka har ta mutu
  • Wata sanarwa daga al'ummar China ta bayyana jimami, bacin rai da kuma mika ta'aziyya ga ahalin Ummita

Jihar Kano - Kungiyar 'yan kasuwa Sinawa a Najeriya (CBCAN) ta bayyana yin Allah wadai da kisan da wani dan kasar China ya yiwa budurwarsa, Ummukulsum Buhari a ranar Juma'an da ta gabata.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba da shawara ga wakilin mutanen China a Kano, Mr Mike Zhang, kungiyar ta ce ta kadu, kuma tabbas ta ji ba dadi da samun labarin aika-aikan da mutumin ya yi.

Wakilin 'yan China ya yi Allah wadai da kisan Ummita
Kungiyar ’Yan China a Najeriya Ta Yi Allah Wadai da Kisan Ummita | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, rahotanni sun karade kafafen yada labarai na yadda wani dan China, Geng Quangrong ya shiga har gida ya caccakawa Ummita wuka ta mutu har lahira.

Mun yi Allah-wadai, inji 'yan China a Najeriya

A sanarwar Allah wadai daga ofishin wakilin na 'yan China, kungiyar ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yan China a Kano na goyon baya dari bisa dari a dauki matakin doka da ya dace."

Hakazalika, kungiyar ta ce mambobinta suna ba da hakuri, kuma tabbas za su ci gaba da zama masu bin doka da oda kamar yadda hukumomi suka tanadar.

A bangare guda, kungiyar ta kuma mika ta'aziyya ga ahalin su Ummita da ma al'ummar jihar Kano baki daya.

Har yanzu 'yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyi da jimami ga mutuwar wannan matashiya.

Yadda Dan China Ya Shiga Har Gida Ya Yiwa Diyata Kisan Gilla, Mahaifyar Ummita

A wani labarin, wani rahoton Daily Trust ya ce, mahaifiyar Ummukulsum Sani Buhari, matashi mai shekaru 23 da wani dan China ya kashe a jihar Kano ta yi bayanin yadda lamarin ya faru.

Idan baku manta ba, a jiya ne Juma'a 16 ga watan Satumba wani tsageran dan China ya shiga har gida ya hallaka wata matashiya a Janbulo ta karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Matashiya wacce aka fi sani da Ummita ta yi karatun unguzoma a makarantar Kano School of Nursing and Midwifery.

Asali: Legit.ng

Online view pixel