Zamfara, Katsina, Osun da Jihohi 10 Na Kashin-Baya a Kokari a Jarrabawar WAEC

Zamfara, Katsina, Osun da Jihohi 10 Na Kashin-Baya a Kokari a Jarrabawar WAEC

  • Hukumar tattara alkaluma ta NBS ta nuna irin abin da makarantun jihohin Najeriya suke tabukawa a jarrabawar WASSCE ta kammala sakandare
  • Sakamakon jarrabawar WASSCE na shekarun 2019, 2020 da 2021 ya nuna jihohin Arewa da na Kudu maso yamma ne suka fi rashin yin abin kwarai
  • Daga cikin jihohin da aka samu raunin dalibai a wadannan shekaru akwai Katsina, Adamawa, da Bauchi, dukkaninsu daga Arewacin Najeriya

Hukumar tattara alkaluma ta kasa wanda aka fi sani da NBS ta fitar da bayani a game da sakamakon jarrabawar WASSCE tun daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Wannan rahoto da hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo a makon nan ya yi bayanin kokarin da dalibai suka tabuka a jihohin Najeriya a jarrabawar.

Hukumar jarrabawa ta WAEC tace a 2020, mutum miliyan 1.53 suka rubuta jarrabawar WASSCE ta kammala sakandare, hakan ya nuna an ragu.

A shekarar 2019, sai da aka yi wa mutane miliyan 1.58 rajista. Daliban da suke yin jarrabawar a makarantun gwamnati sun fi na makarantun kudi yawa.

Kasuwar makarantu na raguwa

A 2021 an ji adadin masu zana jarrabawar sun karu da 1.42%, daga miliyan 1.52 zuwa miliyan 1.53. Punch tace makarantun kudi sun fi samun karuwar mutane.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton yace adadin daliban da aka samu a makarantun gwamnati a 2019 sun zarce 707,000 yayin da aka yi wa mutane 830,756 rajista a makarantun kudi.

Jarrabawar WAEC
Dalibai na jarrabawa Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

A shekarar bana, alkaluma sun nuna masu yin jarrabawar a makarantun kudi sun karu da 2.01% idan har aka kamanta da abin da ya faru a shekarar bara.

Yayin da makarantun gwamnati suka yi wa mutum 838,486 rajista, a makarantu masu tsada na masu cin gashin kansu, an samu masu jarrabawa 721,666,

Zamfara ta zo ta karshe

Da aka tattaro jihohin da suka fi rashin kokari a shekarar bara, Zamfara ce ta zo ta farko. Yawan wadanda suka lashe jarrabawar a jihar ba su kai 10% ba.

An yi amfani da makarantun gwamnati wajen tattaro adadin daliban da ba su lashe akalla darusa biyar a jarrabawar ba, ana hadawa da Ingilishi da lissafi.

1. Zamfara: 9.2%

2. Osun: 32.6%

3. Katsina: 49.2%

4. Kwara: 53.8%

5. Oyo: 54.8%

6. Ogun: 55.2%

7. Yobe: 55.6%

8. Borno: 67.3%

9. Adamawa: 67.6%

10. Bauchi: 67.8%

Legit.ng ta fahimci jihohi bakwai daga cikin jerin sun fito daga Arewa ne, yayin da ragowar uku; Osun, Oyo da Ogun suka fito daga kudu maso yamma.

Ana barin Arewa a baya

Idan aka yi la’akari da yanki, StatiSense tace a nan Arewa ne a baya a shekarar da ta wuce. Daliban yankin Kudu sun fi samun nasara a wannan jarabawa.

1. Kudu maso gabas — 89.8%

2. Kudu maso kudu— 88.1%

3. Arewa maso Tsakiya — 76.5%

4. Arewa maso gabas — 68.1%

5. Kudu maso yamma — 62.9%

6. Arewa maso yamma— 61.5%

Asali: Legit.ng

Online view pixel