Tankin Ruwa Ta Fado Daga Saman Gida, Ya Murkushe Mutum 2 Har Lahira a Legas

Tankin Ruwa Ta Fado Daga Saman Gida, Ya Murkushe Mutum 2 Har Lahira a Legas

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa ta bayyana yadda wani iflia'i ya fado wa wasu mazauna jihar Legas
  • Mutum biyu sun mutu yayin da uku suka raunata lokacin da tankin ruwa ya fado kan wani gida da ke gefe
  • Ana yawan samun irin wadannan lamurra na faduwar gini ko makamancinsa a birnin Legas, Kudu maso Yamma

Bariga, jihar Legas - Rahoton da muke samu daga jihar Legas na bayyana cewa, wani tankin ruwa ya fado ya danne wasu mutane a jihar Legas, inji jaridar The Nation.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta bayyana hakan, inda tace tankin ya danne mutanen biyu ne Ladi Lak da ke Bariga jihar Legas a daren Lahadi 21 ga watan Agusta.

Kodinetan shiyyar Kudu maso Yamma na hukumar NEMA, Ibrahim Farinloye ya tabbatar wa namema labarai faruwar lamarin, inji Daily Nigerian.

Yadda tankin ruwa ya fado kan wani gida, ya murkushe mutane
Tankin ruwa ta fado daga saman gida, ya murkushe mutum 2 har lahira a Legas | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Da yake bayani, Farinloye ya ce tankin ruwan wani bene mai hawa biyu ne ya fado kan wani gidan kasa da ke kusa dashi, ya kashe namiji babba da karamin yaro, kana ya raunata mutane uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, shugabanni a yankin Bariga ne suka kai mutanen da suka samu raunuka ga asibiti kafin zuwan jami’an hukumar agajin gaggawa.

Ana yawan samun irin wadannan hadurra a jihar Legas. Daya daga cikin wadannan hadurra ya faru a watan Oktoban 2023, inda aka yi asarar rayuka sama da 30 a rushewar wani ginin bene.

'Yan Bindiga Sun Yi Watsi da Yarjejeniyar Zaman Lafiya Yayin da Manoma Suka Fara Girbi a Neja

A wani labarin, manoma a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi a jihar Neja sun shiga damuwa yayin da suke fara shirin girbin amfanin gonakansu.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce, manoman sun shiga tashin hankali ne kan warware yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga suka yi a daidai lokacin da tumatir masara da rogo suka nuna.

An sace manoma 16 tsakanin ranakun Asabar da Lahadin karshen makon jiya a kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel