FG: Daraktoci 137 Sun yi Warwas a Jarabawar Neman Karin Girma Zuwa Firinsifal

FG: Daraktoci 137 Sun yi Warwas a Jarabawar Neman Karin Girma Zuwa Firinsifal

  • Wani labari da zai yi wa daliban Najeriya dadi shi ne faduwar warwas din da wasu daraktoci dake kokarin samun aikin gwamnatin tarayya suka yi a jarabawa
  • Wannan ya zo ne bayan wasu ma'aikatan gwamnati 137 sun tsallake jarabawar farko ta kwamfuyuta da aka yi musu, wacce take wani sashi na jarabawar
  • A daya bangaren, ma'aikatan gwamnati 344 ne suke cikin jerin wadanda ya dace su samu shugabannin makarantun sakandaren gwamnatin tarayya 110 dake kasar nan

FCT, Abuja - A kalla mutum 137 daga cikin ma'aikatan gwamnati masu matsayin daraktoci ne suke jiran samun karin girma zuwa matsayin shugabannin makarantun sakandaren tarayya 110 dake fadin kasar nan kuma suka fadi jarabawar da ma'aikatar ilimi ta yi musu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun tarfa jigon APC a yankinsu, sun hallakashi

The Punch ta rahoto cewa, daraktoci 207 wadanda suka tsallake jarabawar da suka yi a na'ura mai kwakwalwa aka ware zasu halarci intabiyu.

Yemi Esan
FG: Daraktoci 137 Sun yi Warwas a Jarabawar Neman Karin Girma Zuwa Firinsifal. Hoto daga Adamu Adamu
Asali: UGC

FG ta jaddada cewa sai an yi jarabawa

Gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin cewa wadanda za su samu karin griman zuwa shugabannin makarantun sakandaren dole su yi jarabawar cancanta kafin su samu nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ma'aikata tayi martani

Kamar yadda jerin sunayen da ya fita a takarda mai lamba FME/S/1317/C.1/VOL.1/51 mai kwanan wata 16 ga Augudtan 2022 kuma daraktan HRM na ma'aikatar ilimi, David Gende ya saka hannu, mutum 207 tun farko aka fitar da cewa sun ci jarabawa cikin mutum 344 da suka rubuta.

Umarnin dake kan takardar yace:

"Wadanda suka yi nasara a jarabawar cancanta da aka yi a ranar 16 ga watan Augustan 2022 ne ake tsammanin zasu gabatar da kansu domin intabiyu."

Kara karanta wannan

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

'Yan Najeriya sun yi martani

'Yan Najeriya sun garzaya shafin Legit.ng na Facebook inda suka dinga martani. Ga wasu daga ciki:

Comr Darlington Ukwuoma yace:

"Ka ji fa, inda shugabannin makarantar sakandare ke faduwa jarabawar."

Agnes Dangiwa ya rubuta:

"Wadanda basu ma rubuta ba sune zasu tsallake."

Haruna Oloruntoba Suliat Yussuf:

"Nufin Allah ne tsallake jarabawa, ba yana nufin wadannan daraktocin basu san komai bane... Ikon Allah ne ke aiki."

Chigozie Coco-b Emma Okonkwo:

"Mutane nawa ne suka je makaranta? Wasu kawai sun je sun dawo."

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

A wani labari na daban, an kara samun bayanai kan mutuwar Sheikh Goni Aisami, fitaccen malamin addinin Islama na Yobe jihar Yobe wanda aka bindige a ranar Juma'a.

Kamar yadda DSP Dungus Abdulkarim, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe ya bayyana, mutum biyun da ake zargi sojoji ne daga bataliya ta 241 sake Recce a Nguru sun shiga hannu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Matar Gwamna Mummunan Farmaki

Daily Trust ta rahoto cewa, yace lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan Aisami ya ragewa daya daga cikin wadanda ake zargin hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel