Uba Ya Fusata, Ya Garkame Shagon Diyarsa da Ta Ki Tafiya Italiya Yawon Karuwanci

Uba Ya Fusata, Ya Garkame Shagon Diyarsa da Ta Ki Tafiya Italiya Yawon Karuwanci

  • Wani mahaifi ya garkame wajen sana’ar diyarsa na gyaran gashi saboda ta ki yarda a kaita Turai yin karuwancin
  • Mahaifin har ya yi barazanar tsinewa yarinyar idan har bata tafi kasar Italiya ta nemo masu kudi ba
  • Hukumar da ke yaki da safarar mutane ce ta bayar da wannan labari mai ban al’ajabi a lokacin wayar da kan jama’a a jihar Edo

Jihar Edo - Hukumar da ke yaki da safarar mutane a Najeriya (NAPTIP) ta bayyana yadda wani uba ya rufe shagon gyaran gashi na diyarsa saboda ta ki yarda ayi fataucinta zuwa kasar Italiya, rahoton Daily Trust.

Shugabar hukumar NAPTIP, Dr. Fatima Wazir-Azi, ta bayyana haka yayin wani shiri na wayar da kan jama’a tare da samar da mafita a kan fataucin mutane a garin Idunmwuniye, jihar Edo, da hadin gwiwar tawagar Sarkin Benin kan safarar mutane.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

Yadda uba ya garkame shagon diyarsa saboda ta ki tafiya yawon karuwanci
Uba Ya Fusata, Ya Garkame Shagon Diyarsa da Ta Ki Tafiya Italiya Yawon Karuwanci | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Dr Waziri wacce ta samu wakilci kwamandan NAPTIP reshen jihar Edo, Bar. Nduka Nwanene, ta ce an shirya taron ne don samar da mafita mai dorewa da aiwatar da tsare-tsare don magance matsaloli masu alaka da fataucin mutane da kaura mai hatsari a jihar.

Yadda lamarin ya faru

A cewar NAPTIP:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mahaifin wanda aka sakaya sunansa ya kira diyarsa cewa ya kammala duk wani shiri don tafiyarta Italy da kuma samowa iyalin kudi amma tace sam ba za ta ba.
“Sai mahaifin ya fusata sannan ya garkame shagonta na gyaran gashi ya kuma yi barazanar sallamawa duniya ita tunda taki zuwa nemo masu kudi.
“Iyaye su daina matsawa yaransu yin wannan tafiya mai hatsari saboda rayuka da dama sun lalace da sunan zuwa nemawa iyaye kudi a kasar waje.
“Ba wai muna cewa kada mutane su je kasar waje bane, kowa na da yancin yin tafiya amma dole ayi tafiya mara hatsari da takardun da suka dace don kada aje a tatse ka sannan a tursasa maku zama bayi, karuwai da yin ayyuka masu wahala.”

Kara karanta wannan

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

Ta ce hukumar NAPTIP na hadaka da masarautun gargajiya da garuruwa saboda masu fataucin mutane sun mayar da hankali kan garuruwan kakkara yayin da har yanzu mutane da dama basu san da hatsarin da ke tattare da fataucin mutane da kaura ba bisa ka’ida ba.

Shugabar NAPTIP din ta kuma ce an shirya taron ne musamman saboda garuruwa irin su Idunmwuniye, Odogbo, Obagie, Ewesie, Ehor, Igieduma, Ogan, Ugoneki da Abudu a kananan hukumomin Ikpoba-Okha, Uhunmwode da Orhionmwon.

Ta kuma ce za su zanta da manyan masu fada aji irin Shugabannin mata, kungiyoyin yan banga, mawaka, Shugabannin addinai, san-kira, malaman makaranta, dalibai da matasa.

A karshe ta jinjinawa Sarkin Benin, Oba Ewuare II, kan kafa tawagar tsaro kan fataucin mutane da kuma tsinewa masu fataucin mutane wanda ya sanyaya gwiwar masu fataucin mutane a fadin jihar.

Ba ma goyon bayan safarar mutane

A nasa bangaren, wakilin sarkin Benin, Cif Isaac Oghafua Oyeoba, Oyeoba na Benin, ya ce Basarake na Benin da fadar masarautar duk suna adawa da fataucin mutane.

Kara karanta wannan

Buhari ga jami'ai: Ku tabbata kun kawar 'yan ta'addan Najeriya gaba daya

Ya ce daga cikin matakan magance lamarin, fadar masarautar ta kafa wata kungiya mai zaman kanta da ke kula da yan hijira da suka dawo, ana horar dasu sannan a sake sama masu wajen zama da hadin gwiwar gwamnati.

Hakazalika da yake jawabi, wani matashi a garin, Mista Osasere Osawaru, ya alakanta lamarin da talauci da rashin aikin yi sannan ya roki gwamnati a dukkan matakai da su bayar da fifiko wajen samawa matasa aikin yi don magance lamarin.

Kamar Almara: Kyakkyawar Budurwa Ta Wallafa Sakonnin Soyayya Da Mai Gadinta Ya Tura Mata Ta WhatsApp

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna Temitope Akinrimisi ta koka a shafin Twitter bayan mai gadinta ya fallasa irin son da yake mata.

Temitope ta ce ta cika da mamakin samun sakon soyayya a WhatsApp daga mai gadinta.

A sakonnin da ya wallafa a Twitter, mai gadin ya ce ta dade tana burge shi amma a yanzu ba zai iya ci gaba da boye sirrin a zuciyarsa ba.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Damar Saduwa da Ni, Matar Aure Ta Faɗa Wa Kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel