Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya

Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya

Matasan Najeriya a lokuta daban-daban sun nunawa duniya cewa kasar tana da albarka da dimbin masu hazaka.

Sun kafa tarihin da ba a taba tunanin zai yiwu ba a makarantun su daban-daban.

Kafin su zama cikakkun abin misalai ga mutane da yawa, wasu daga cikinsu da farko sun rinjayi fargabar su kuma suka tsaya tsayin daka don cimma burinsu.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi duba ga wasu matasa 'yan Najeriya biyar da suka yi gagarumin abin a zo a gani a makarantu daban-daban.

1. Ruqayyah Adelakin

Ruqayyah bata taba yunkurin kafa tarihi a LAUTECH ba. Abin da ya ja hankalinta sosai shine sakamakon ta na ajin farko a jami'ar. Yayin da take bibiyar burinta, sai ta mike hanya dodar.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

Tare da labarin cewa sashin nazarin halittu ba ta taba samar da mai digiri da sakamakon farko ba, kusan ta shagala tare da cire rai. Kokarinta daga baya ya ci nasarar kafa tarihin da ba a taba yi ba a sashin tsawon shekaru 19.

2. Halima Yayajo

Halima ta tara jimillar kyaututtuka tara lokacin da ta kammala karatu daga Jami'ar Jihar Gombe. Ta kuma fito a matsayin daliba mafi kwazo a sashin ta.

Daga cikin kyaututtukan da ta samu sun kasance na daliba mafi kwazo a ilimin kimiyyar halittu na likitanci, histopathology, likitancin al'umma, da kuma fannin magunguna.

3. Fatima A. Akinola

Matashiyar 'yar Najeriya ta kammala karatu daga Jami'ar Marshall da ke Amurka tare da cikakken maki na 4.0/4.0 kuma an yi bikinta sosai a gida da waje.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar UNIMAID

Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya
Fatima A. Akinola | Hoto: LinkedIn/Fatima Akinola
Asali: UGC

Kafin wannan rawar da ta taka, ta kasance a 2017 daliba mafi kwazo da ta kammala karatu daga Jami'ar Usman Danfodiyo yayin da ta kafa tarihin da ba a taba yi ba shekaru sama da 42.

4. Ofure Ebhomielen

Labarin Ofure shine babban labari mai daukar hankali. Yayin da take karatun digiri na farko a Jami'ar Ibadan, ta kafe makinta na CGPA da ya kai 7.0 har ta kammala. Wannan ya sanya ta zama daliba mace ta farko da ta taba yin hakan.

Bayan digiri na farko, ta ci gaba da zuwa Amurka kan tallafin karatu da ta samu. Ta ce ilimin da ake samu a kasashen waje ya fi abin da ake samu a gida Najeriya.

5. Mary Jesulade

Mary mai shekaru ashirin da daya ita ma ta kafa tarihi a LAUTECH. Mary ta ce tuni ta ji labarai daban-daban game da sashen da ta yi karatu tun kafin ta fara karatu.

Kara karanta wannan

Hotunan dan shekara 61 da ya auri yarinyar da ya raina a hannunsa, an yi cece-kuce

Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya
Mary Jesulade | Hoto: LinkedIn/Mary Jesulade
Asali: UGC

Duk lokacin da dalibin aji na farko ya yi sanyin gwiwa, ko yaushe tana gaya wa kanta:

"Mutane ko yaushe za su fadi ra'ayinsu kan batutuwan da suka shafi lamarin, amma ya rage gare ku ku sarrafa wadannan ra'ayoyin ta hanya mafi kyau da za ku iya kuma ku tabbatar da su daidai ne ko kuskure."

Sojin sama ta dawo da shirin daukar daliban sakandare kai tsaye zuwa aikin soja

A wani labarin, Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta sake gabatar da shirin daukar daliban da suka kammala makarantar sakandare ta soji kai tsaye a matsayin sojan sama, The Guardian ta ruwaito.

Babban Hafsan Sojojin Sama (CAS), Air Marshall Isiaka Amao ne ya bayyana hakan, a wurin faratin yaye dalibai na 36 na Makarantar Sojojin Sama da ke Jos ta Jihar Filato.

Amao ya ce wasu daga cikin daliban da suka nuna sha’awa kafin su shiga cikin shirin daukar kai tsaye an tura su rundunonin NAF daban-daban a fadin kasar bayan sun sami horo a Cibiyar Horar da Sojoji da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

Asali: Legit.ng

Online view pixel