Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo

  • Wasu mahara da ake zaton mambobin kungiyar IPOB ne sun kai farmaki fadar sarkin Etekwuru da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo
  • 'Yan bindigar sun cinna wa fadar sarkin wuta tare da motarsa da wasu kayayyaki
  • Lamarin ya afku ne a daren ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba

Imo - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mambobin kungiyar IPOB ne sun sanya wuta a fadar sarkin Etekwuru da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema na jihar Imo.

An kuma tattaro cewa maharan sun kuma kona wata babbar motar highlander jeep da sauran kayayyaki a yayin kaddamar da harin.

Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo
Ana wata ga wata: ‘Yan bindiga sun cinna wuta a fadar sarkin Imo Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto daga majiyoyi cewa lamarin ya afku ne a daren ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke bayan sojoji sun bindige 'yan kungiyar awaren IPOB har 5

Rahoton ya nuna cewa bayan sun mamaye fadar sarkin, sai suka fara nemansa, da basu gan shi ko wani daga cikin ahlinsa ba, sai kawai suka cinna wa fadar wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiya ta bayyana cewa a yanzu haka basaraken yana samun mafaka a hedikwatar 'yan sanda da ke Mmahu.

Duk a jiyan, jaridar Daily Sun ta rahoto cewa, an samu tashin hankali a Arochukwu ta jihar Abia a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba yayin da jami'an tsaro ke fafatawa da 'yan kungiyar awaren IPOB a yankin.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa mutane hudu da ake zargi 'yan kungiyar IPOB ne ana fargabar an kashe su a yayin fafatawar.

Yan bindiga sun sake kai hari ofishin yan sanda, sun saki fursunoni

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

A wani labarin kuma, wasu yan bindiga da ake zargin yan ta'addan IPOB/ESN ne sun kuma kai hari ofishin yan sanda a inda suka banka wuta hedkwatar yan sandan karamar hukumar Isiala Mbano.

Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai hari ofishin dake unguwar Umuelemai ne yayinda ake ruwan sama cikin daren Alhamis, 21 ga Oktoba, 2021.

An tattaro cewa yan sandan dake wajen sun arce da kafafunsu yayinda yan bindigan suka bude musu wuta, riwayar Sahara Reporters.

Asali: Legit.ng

Online view pixel