Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya

  • Mai sarautar gargajiya a jihar Yobe ya narkawa gwamna Buni ashariya, ya hadu da fushin gwamna
  • Rahoto ya bayyana cewa, tuni aka aikowa da hakimin takardar kora wacce ta bayyana irin laifukansa
  • Bincike ya bayyana yadda lamarin ya faru, har ta kai ga kama hakimin nan take tare da tsare shi a wajen 'yan sanda

Yobe - An dakatar da Hakimin Gabai a masarautar Gujba ta jihar Yobe bisa zargin fadin "kalaman batanci, da rashin da'a, da rashin biyayya da rashin mutunci" ga Gwamna Mai Mala Buni.

An kawo dakatarwar ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren masarautar Mohammed Ali Yusuf, The Nation ta ruwaito.

Hakimi a Yobe ya hadu da fushin gwamna bayan da ya narkawa gwamnan ashariya
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Takardar dakatarwa mai lamba GEC/BUNI/ADM/VOL-1-27 mai kwanan wata 18 ga Oktoba 2021 ta karanta:

Kara karanta wannan

Muna farin cikin soke dokokin COVID-19 a Masallacin Makkah da Madina: Hukumar jin dadin Alhazai

“Majalisar Masarautar Gujba ce ta umurce ni da in rubuta kuma in sanar da kai ta wannan wasikar cewa hidimar ka da Majalisar Masarauta a matsayin Hakimin Gundumar Gabai an dakatar da kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

”Dakatarwar ta biyo bayan maganganun ka marasa kyau, babban rashin da’a, rashin biyayya da rashin girmama hukuma da aka kafa.
“A saboda wannan dalilan kuma saboda dabi’ar ka, Majalisar Masarautar Gujba ta yanke shawarar kuma ta dakatar da nadinka daga yau 18 ga Oktoba 2021 har zuwa wani lokaci da jiran bincike kan lamarin.
"An kwafi wannan wasikar zuwa ga Maigirma Kwamishinan Ma'aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu da Shugaban Karamar Hukumar Gulani don karin bayani da karin mataki."

Duk da wasikar dakatarwar ba ta bayyana yanayin cin mutuncin da ake zargin ba, binciken ya nuna cewa Hakimin ya yi ruwan ashariya ne a kan Buni lokacin da ADC na Gwamnan ya nemi ya cire hannayensa daga aljihunsa kafin musayar musabaha da Gwamnan.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin Buhari: Za a sayi janareta na N104bn, aikin wutar Mambila kuma N650m

Wani shaidan gani da ido ya shaida cewa ya ki amincewa da bukatar ADC din cikin rashin mutunci tare da zagi a idon Gwamnan.

Binciken da aka yi ya nuna cewa an kama shi nan take kuma an tsare shi a ofishin 'yan sanda kan lamarin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Yobe ASP Dungus Abdulkareem ya ce bai san da lamarin ba lokacin da aka tuntube shi.

'Yan bindiga sun sako sarkin Bunguda na Zamfara bayan shafe kwanaki a hannunsu

Wani sarki kuwa, kwanaki sama da 30 bayan sace shi, Sarkin Bungudu ta jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru, ya sake samun 'yanci daga hannun 'yan bindiga.

A baya mun ruwaito muku cewa, an yi garkuwa da sarkin ne yayin da wasu 'yan bindiga suka dira wa ayarin motocin sa a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 14 ga watan Satumba.

Rahoton Daily Trust ya ce, wata majiyar tsaro ta ce an saki sarkin ne da yammacin ranar Asabar a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya koka kan yadda wasu ke harin rayuwarsa

A wani labarin, Hukumar jin dadin alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa da yardar Ubangiji bana maniyyata a Najeriya zasu samu zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajji.

Wannan ya biyo bayan soke dokokin kariya daga cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Saudiyya tayi a farkon makon nan.

Kwamishanan hukumar mai wakiltar al'ummar yankin kudu maso kudu, Musa Sadiq Oniyesaneyene, a hirarsa da Legit Hausa ya bayyana cewa ko makonnin baya ya shiga Saudiyya kuma da yardar Allah bana za'a tafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel