Hotunan dan shekara 61 da ya auri yarinyar da ya raina a hannunsa, an yi cece-kuce

Hotunan dan shekara 61 da ya auri yarinyar da ya raina a hannunsa, an yi cece-kuce

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar hotunan wasu ma'aurata a shafukan soshiyal midiya
  • Angon wanda ya kasance dattijo mai shekaru 61 a duniya ya auri yarinyar da ya raina a hannunsa bayan ta cika shekaru 18
  • Sai dai ma'auratan sun bukaci masu tsegumi kansu da su fuskanci matsalolin gabansu maimakon sanya masu ido

Wani dattijo mai shekaru 61 da aka ambata da suna Michael Haugabook, ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya auri budurwa ‘yar shekaru 18 mai suna Deja.

An tattaro cewa Micheal wanda ke da haihuwar ‘ya’ya uku, ya kasance daga cikin wadanda suka yi dawainiya da Deja tun daga lokacin da ta zo duniya.

Hotunan dan shekara 61 da ya auri yarinyar da ya raina a hannunsa, an yi cece-kuce
Hotunan dan shekara 61 da ya auri yarinyar da ya raina a hannunsa, an yi cece-kuce Hoto: lindaikejiblogofficial
Source: UGC

A daya daga cikin hotunan da shafin Instagram na lindaikejiblogofficial ya yada, an gano dattijon dauke da matar tasa a hannunsa a lokacin da take ‘yar karamar yarinya.

Read also

Bayan matsalar kwanakin baya, Kamfanin Facebook na shirin sauya suna

An kuma rahoto cewa a lokacin da ta bata a 2017, yana daga cikin wadanda suka dunga rokon mutane da su taimaka wajen nemo ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, a lokacin da take da shekaru 17, Deja ta wallafa a shafinta cewa tana soyayya da wani amma mutane basu san ko wanene ba.

Da ta cika shekaru 18, sai ta auri Michael, wannan ya sa mutane na ta tunanin dama chan rainonta yake yi sannan ya dunga soyayya da mahaifiyarta zuwa lokacin da za ta isa aure.

Banbancin shekarun dake tsakaninsu ya sa mutane cece-kuce da kuma kasancewarsa ubangidanta. Mutane na al’ajabin dalilin da zai sa dattijo kamar wannan ya auri ‘yar shekara 18.

Wata takarda na kamun da aka yiwa Micheal a shekarar 2014 ya nuna cewa shekarunsa 54 a waccan lokacin, hakan na nufin shekarunsa 61 a yanzu.

Read also

Da gaske Buhari Jibril ne na Sudan? A karshe Femi Adesina ya fayyace gaskiya

Deja na da yarinya ‘yar shekara daya kuma ita ce ke kula da yaran dattijon guda uku duk da karancin shekarunta.

Sai dai kuma ma’auratan sun yi wa mutane hannunka mai sanda, inda suka ce kowa ya ji da abun da ke gabansa, maimakon tsegumi a rayuwar wasu.

Martanin jama’a kan lamarin:

nekkycutie ta ce:

“Wannan auren mara tsafta ba zai kai ko ina ba! Kwanan nan idonta zai bude don haka zai fi a kyale ta ta gano komai da kanta."

chinnycee ta yi martani:

“Banbancin shekaru da girman jikin abun haushi ne ."

jennycalis ta ce:

"Tambaya daya: Ina mahaifiyar yarinyar?"

Kotu ta hukunta wata mata dake duba wayar mijinta ba tare da izini ba

A wani labarin, wata kotu a haɗaɗɗiyar dauƙar Larabawa (UAE) ta yankewa wata mata hukuncin zaman gidan kaso na tsawon wata uku saboda duba wayar mijinta ba tare da izini ba.

Read also

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

Aminiya Hausa ta rahoto cewa mijin ya kai ƙarar matar ne gaban kotu, domin a bi masa haƙƙinsa na duba wayarsa da take yi ba tare da neman izini ba.

Rahotanni sun bayyana cewa kotun dake zamanta a yankin Ras a Al-Khaima ta kama matar dumu-dumu da laifin keta sirrin mijinta.

Source: Legit

Online view pixel