Latest
Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana abubuwan da ke burgeta a kan mai martaba Muhammadu Sanusi bayan sun yi wata haduwar ba zata a filin jirgin sama.
Sabon farashin fetur daga matatar Dangote ya sa ‘yan kasuwa sun kauce wa manyan rumbun ajiya na masu zaman kansu, yayin da ake sa ran ci gaba da saukar farashin.
Rashin wutar lantarki ya shafi Bayelsa da Rivers, inda mutane ke fama da wahala sakamakon lalata turakun wuta na layin Owerri-Ahoada da ke ba jihohin wuta.
Hukumar Kwastam ta kama dala $1.1m da Riyal 135,900 a Kano, a cikin wani fatikin dabino. Kotu ta ba da umarnin a kwace kudaden tare da mika su ga gwamnati.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci masoyansa su biyo shi shafin TikTok domin yada tunaninsa game da siyasar Najeriya da jam’iyyarsu ta SDP.
Mallam Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Kaduna da tsare Jafaru Sani bisa laifin da ba na hurumin jihar ba. Tsohon gwamnan ya yi Allah ya isa kan kama Jafaru.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun tursasa mutane zuwa cikin daji.
Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi magana kan matsayarsa a APC inda ya jaddada cewa har yanzu mamba ne na jam’iyyar kuma yana son a dinga kiransa haka.
Majalisar Wakilai ta amince da kudirorin haraji, ta soke bukatar karin VAT, ta samar da sabuwar Hukumar Haraji ta Najeriya, tare da kafa kotun korafe-korafen haraji.
Masu zafi
Samu kari