Wata Sabuwa: Tsohon Gwamna El-Rufai Ya Zargi 'Yan Sanda da 'Sace Kwamishina'
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce wasu da ke ikirarin ‘yan sanda ne sun sace tsohon kwamishinansa, Jafaru Ibrahim Sani
- El-Rufai ya ce an garkame Malam Jafaru a kurkuku ba tare da sahihan takardu daga ‘yan sanda ko ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna ba
- Ya ce ana tuhumar Jafaru da safarar kuɗi, wanda laifi ne na tarayya, amma ya ce an tsare tsohon kwamishinan ne saboda ya fice daga APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya yi maganganu masu zafi da kotu ta garkame tsohon kwamishinan jihar a lokacin mulkinsa.
El-Rufai ya yi ikirarin cewa wasu 'yan tawagar masu ƙwamushe mutane bisa sahalewar Uba Sani ne suka yi awon gaba da Mallam Jafaru Sani.

Asali: Twitter
An kulle tsohon kwamishinan Kaduna a kurkuku
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, El-Rufai ya yi karin haske da cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abokin aikimu kuma ƙwararren tsohon kwamishina a lokacin mulkin El-Rufai, Malam Jafaru Sani, an sace shi a Kaduna da rana yau!
"Tawagar masu garkuwa da mutane ta Uba Sani, da ke ikirarin su 'yan sanda ne suka yi garkuwa da shi."
Tsohon gwamnan na Kaduna, ya ci gaba da cewa wata kotun majistare ta ba da ajiyar Malam Jafaru a gidan yari ba tare da rahoton 'yan sanda ba.
"An tasa keyar Jafaru zuwa gidan yari bisa umarnin alkalin kotun majistare ba tare da rahoton farko na ‘yan sanda ko tuhuma daga ma’aikatar shari’a ta jiha ba."
- Nasir El-Rufai.
"Gaskiyar laifin da Jafaru ya yi" - El-Rufai
Mallam Nasir El-Rufai ya ce da suka bincika, sai suka gano cewa ana zargin Jafaru da safarar kudin haram, wanda ya ce ba hurumin jiha ba ne daukar mataki kan irin wannan laifi.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa:
"Bayan bincike, mun gano cewa ana tuhumar Jafaru da safarar kuɗi, wani laifi na tarayya da kotunan jiha ko ma ‘yan sanda ba su da hurumin bincike ko yanke hukunci a kai."
Amma El-Rufai ya yi ikirarin cewa an kama Jafaru tare da garkame shi a kurkune kawai saboda ya fice daga APC, ya koma jam'iyyar SDP.
"Gaskiyar “laifin” Jafaru ita ce ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP, tare da kasancewarsa wanda aka gabatar a matsayin ɗan takarar minista mai wakiltar Kaduna a watan Agustan 2023."
- Nasir El-Rufai.
El-Rufai ya alakanta kama Jafaru da na Bashir

Asali: Twitter
A yanayin salon da aka kama tsohon kwamishinan, El-Rufai ya yankewa kansa hukuncin cewa:
"Wannan dabara tana kama da wadda aka yi amfani da ita kan wani abokin aikinmu, Bashir Saidu, lokacin da aka sace shi a ranar 31 ga Disamba, 2024, aka tsare shi na tsawon kwanaki 50 kafin a sako shi bisa beli.
"Rashin gaskiya da kwanta-kwantar da wasu alkalan majistire da na babbar kotu ke yi a tsarin shari’ar Kaduna yana da matukar tayar da hankali.
"Muna gani kuma muna jira, domin babu wata doka ko matsayi da ke dawwama. Kuma za a tambayi kowa game da ayyukansa, tabbas ranar kin dillanci na zuwa."
Kalmar karshe da El-Rufai ya rubuta ita ce:
"Allah ya isa! Allah ya tsine ma su"
ICPC ta gurfanar da Bashir Sa'idu a kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar ICPC ta gurfanar da Alhaji Bashir Sa’idu, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna a zamanin Nasir El-Rufai.
An gurfanar da shi ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda ake zargin sa da sama da fadi da kuɗaɗen gwamnati a lokacin yana aiki karkashin El-Rufai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng