Latest
A kalla mutane shida ne babbar mota dauke da yashi ta mitsike sakamakon tsinkewar birki a kan babban titin Gubio dake wajen babban birnin Maiduguri a Borno.
Gwamnan jihar RIvers, Barrista Nyesom Ezenwo Wike, ya sake nada sabbin mutane 100,000 matsayin hadimai na musamman da zasu yi masa aiki lokacin zaben 2023.
Kotun Amurka ta yi hukunci kan dan damfarar nan da ya yi fice, Hushpuppi bayan da ya amsa laifin sace kudin jama'a. Zai yi zaman magarkama na tsawon shekaru 11.
Wani ‘Dan Najeriya a Ingila ya Koka da ya cika tankin tankin mota a kan N60000. A Najeriya wannan kudi ya isa kamfani ko gwamnati ta albashin ma’aikata biyu.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da hakimin kauye, suna barazanar kakaba haraji kan manoma idan ba a ba su kudin fansan da suke bukata a kan lokaci.
Legacy Logistics LLC Ltd sun yi da’awar taimakawa Atiku Abubakar da biza. Lauyoyin kamfanin sun fara maganar kai shi kotu idan bai fito masu da hakkinsu ba
Shugabar mata ta jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, ta ce sam babu shugabanci nagari a PDP, dole ta sauya sheka.
Dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a jam'iyyar Labour ya bayyana abin da zai fi mai da hankalinsa a kai idan ya samu damar gaje kujerar Buhari a 2023.
Dan majalisar tarayya na Kano, Hon Ado Doguwa ya karyata rahoton da wani kafar watsa labarai na intanet ya wallafa na cewa ya ce zai tona wa Ganduje asiri.
Masu zafi
Samu kari