Bayan Zuba Soyayyar Shekaru 2 Cikin Talauci, Saurayi Yayi Kudi Tare da Auren Wata

Bayan Zuba Soyayyar Shekaru 2 Cikin Talauci, Saurayi Yayi Kudi Tare da Auren Wata

  • Wata budurwa mai suna Oghadeva Sandra ta bada labarin mummunan abinda ta fuskanta na cin amanarta da saurayinta yayi bayan shekaru biyu
  • Sandra tayi ikirarin cewa sun yi soyayya mai zafi da matashin yayin da yake ta fama da talauci amma ya aure wata bayan ya samu arziki
  • A yayin bayyana takaicin ta a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa duk da yayi aure ya cigaba da aika mata sakon cewa yana son ganinta

Oghadeva Sandra ta bada labarin yadda wani matashi da suka kwashe shekaru biyu suna zuba soyayya da shi yayi watsi da ita ya aura wata bayan ya samu arziki.

Saurayi da Budurwa masoyan juna
Bayan Zuba Soyayyar Shekaru 2 Cikin Talauci, Saurayi Yayi Kudi Tare da Auren Wata. Hoto daga @sandra0ghe, Getty Image
Asali: UGC

Sandra ta tuna yadda ta dinga hakuri da shi yayin da suke soyayya kuma a hakan har suka kwashe shekaru biyu tare duk da bashi da komai.

Kara karanta wannan

Akwai Sakayya: Budurwa Ta sanar da Yadda Saurayinta Na Shekara 5 Ya Auri Balarabiya

Abun takaicin shi ne, yana fara samun kudi yayi watsi da ita kuma ya aure wata daban.

A yayin bayar da labarin mai cike da takaici a Twitter, Sandra tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na yi soyayya da matashin da bashi da ko sisi na shekaru biyu duk da yana bin wasu matan amma ban damu ba. Yana samun kudi ya aure wata. Yanzu wacce irin shawarar zaku bani?
“Duk da yana da auren kuma yana cigaba da yi min magana wasu lokuta. A wani lokacin har yana cewa yana son gani na. Na ki dai, idan da ni mutuniyar banza ce me zai sa ya neme ni?”

Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu

“Zan iya rantsuwa cewa shekaru biyun da kuka yi tare ke ma kin dinga cin amanarsa kina tsammanin bai sani ba. Shiyasa ya ki auren ki.”

Kara karanta wannan

Matashi Ya Halaka Mahaifin Budurwarsa Mai Shekaru 68 a Bauchi

Muhphasa yace:

“Manta da shi Sandra, kin kaucewa harsashi ne kuma ba dole ki gane hakan ba. Ubangiji ya baki wanda ya fi shi.”

Top Notch yace:

“Namiji ya san inda zuciyarsa tafi karkata, ta yuwu a gado kawai ki ke da kwazo da nishadi, amma baki da nagartar da yake so a matarsa ta aure.”

Arc Baby tayi martani da cewa:

“Yallabai ba sai ka yi bayani ba saboda ku maza kun iya kare kan ku.”

Eketter yace:

“A gaskiya wasu suna da kirki. Yanzu har magana ki ke wa sakaran? Me yasa kike da kirki haka?”

Ga wallafar a Twitter:

Akwai Sakayya: Budurwa Ta sanar da Yadda Saurayinta Na Shekara 5 Ya Auri Balarabiya

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwar Najeriya mai amfani da suna @SandraOse_ tayi suna a yanar gizo bayan ta bada labarin yadda saurayinta mai suna Izuchukwu ya rabu da ita bayan kwashe shekaru biyar suna zuba soyayya.

Tayi wallafa ne yayin yin martani ga mai wasan barkwanci Taaooma da yace jama’a su bayar da labarin cin amanarsu da aka taba yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel