Borno: Matasa Sun Balle Zanga-zanga Sakamakon Mutuwar Mata 6

Borno: Matasa Sun Balle Zanga-zanga Sakamakon Mutuwar Mata 6

  • Fusatattun matasa sun tayar da zanga-zanga tare da rufe babban titin Gubio zuwa Maiduguri dake jihar Borno sakamakon mutuwar wasu mata shida
  • An gano cewa matasan sun fusata ne bayan wata babbar mota ta murkushe wata mota dake dauke da mata shida zasu je gona, hakan yayi ajalinsu
  • Lamarin ya faru ne bayan da babbar motar tayi yunkurin wuce tifar dake dauke da matan shida, hakan ya ja ajalinsu

Borno - A kalla mutane shida ne babbar mota dauke da yashi ta mitsike sakamakon tsinkewar birki a kan babban titin Gubio dake wajen babban birnin Maiduguri a jihar Borno.

Babbar mota
Borno: Matasa Sun Balle Zanga-zanga Sakamakon Mutuwar Mata 6. Hoto daga TheCable.ng da thenationonlineng.net
Asali: UGC

Lamarin ya auku wurin karfe 10:05 na safiya a Kaswan Fara dake Shagari Lowcost Estate a Maiduguri da safiyar Juma’a.

Yadda lamarin ya faru

Wani ganau mai suna Kola Fatai ya sanar da Daily Trust cewa babbar motar yashin ta ci karo da mota budaddiya dauke da matan wadanda zasu tafi gona, kuma a take ya halaka su shida.

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin yankin mai suna Iman Buba, ya sanar da Daily Trust ta wayar salula cewa an bankawa manyan motoci biyu wuta kuma fusatattun matasa ne suka yi hakan yayin da ‘yan sanda ke kokarin kwantar da tarzomar.

Tuni fusatattun matasa masu zanga-zanga suka rufe babban titin Gubio zuwa Maiduguri, jaridar TheCable ta rahoto.

Wani ganau ya sanar da cewa babbar motar wacce ta kawo wannan hatsarin tayi yunkurin wuce wata tifa ce, amma ta rasa birki tare da fadawa motar dake dauke da matan.

Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 5 a jihar Kogi

A wani labari na daban, Kimanin rayukan mutane biyan ne suka salwanta yayin aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kauyen Ogbabo dake kan babbar hanyar Ajaokuta a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Tsere A Yayin Da Yan Bindiga Suka Sace Fasinjoji 9 A Babban Jihar Najeriya

Mista Olusegun Martins, shugaban hukumar kula da tsaron manyan hanyoyi, shine ya tabbatar da wannan lamari yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya, inda ya ce akwai kimanin mutane biyu da suka jikkata a hatsarin.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hatsari ya auku ne da misalin karfe 3.30 na yammacin ranar Juma'ar da ta gabata wanda ya hadar da wasu motoci biyu kirar Toyota Sienna mai lambar EPE 307 XU da kuma wata motar mai lambar AK ILIKA 1 tare da tambarin NAOWA (Nigerian Army Officers Wives Association).

Asali: Legit.ng

Online view pixel