Rikici ya shiga tsakanin Atiku da Wani Kamfani Kan $5.9m na Bizar Amurka a 2018

Rikici ya shiga tsakanin Atiku da Wani Kamfani Kan $5.9m na Bizar Amurka a 2018

  • Kamfanin Legacy Logistics LLC Ltd yace ta hannunsa Atiku Abubakar ya samu zuwa Amurka a 2018
  • Duk da an yi hanyar da Atiku ya samu takardar shiga kasar wajen, kamfanin yace ba a biya sa kudinsa ba
  • Lauyoyin Legacy Logistics LLC Ltd sun fara maganar zuwa kotu idan ba a fito masu da hakkinsu ba

Abuja - A yayin da aka kada gangar siyasar 2023, Atiku Abubakar mai neman takara a jam’iyyar PDP ya samu kan shi a rikici game da biza tun na 2018.

The Nation ta kawo rahoto cewa wani kamfani Legacy Logistics LLC yana zargin Atiku Abubakar da kin biyansa kudinsa bayan ya nemo masa biza.

Kamfanin yayi ikirarin ta hannunsa ‘dan takarar shugaban kasar ya samu takardar shiga Amurka, amma bai biya sa kudinsa, fam Dala miliyan 5.9 ba.

Kara karanta wannan

PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

Legacy Logistics LLC Limited yace an bukaci ‘dan siyasar ya biya wadannan kudi, amma ya ki cika alkawarin da aka yi, a yau shekaru hudu kenan.

Kudi suke nema wurinsu Atiku

Farfesa Maxwell Gidado (SAN) wanda shi ne Mai taimakawa Atiku Abubakar wajen harkokin shari’a ya musanya zargin da wannan kamfani yake yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya nuna Legacy Logistics LLC ya ambaci Maxwell Gidado a matsayin wanda ya san da yarjejeniyar, lauyan yace sam babu wannan maganar.

Atiku Abubakar a Amurka
Atiku Abubakar a gidan jaridar VOA Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

A cewar Farfesa Maxwell Gidado, ba kamfanin Legacy Logistics LLC Ltd suka nemawa Atiku biza ba, kuma ba ayi da su za a biya su $5.9m ba.

Kamar yadda ya fada, Hadimin yace an samu bizar kasar wajen ne ta hannun wani Ambasada Kumba, kuma abin da aka kashe bai zarce $500, 000 ba.

Farfesan yace kamfanin ya rubuta wasika ne domin ya tatsi kudi daga hannun Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Sarakuna 17 Sun Yi Watsi da Atiku, Sun Karyata Batun Goyon Bayan Takararsa

Za a iya karewa a kotu

Lauyoyin wannan kamfani sun fitar da takarda a karshen Satumban 2022, suna cewa idan har ba a biya su kudin da suka kashe ba, za su kai maganar kotu.

Saharareporters ta rahoto cewa Legacy Logistics LLC Ltd sun yi da’awar sun shiga sun fita domin Atiku Abubakar da tawagarsa su iya zuwa kasar Amurka.

An kai karar 'Dan majalisar Kano

Wani Bawan Allah da yake aikin jarida a Kano, Abdullahi Yakubu ya dauki hayar Lauyoyi, ya shigar da karar Hon. Alhassan Ado Doguwa a gaban Alkali.

Abdullahi Yakubu yace daga kokarin lallashin ‘Dan majalisar tarayyan, sai ya ji saukan duka a kunnensa wanda hakan ya jawo yana ta rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel