Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Sahihin Dan Takaran Gwamnan APC a Kaduna

Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Sahihin Dan Takaran Gwamnan APC a Kaduna

  • Kotu ta yi watsi da karar da Hanarabul Sani Sha'aban ya shigar don soke zaben fidda gwanin gwamnan Kaduna
  • Sha'aban ya shigar da kara kan zargin murdiyan sunayen deleget lokacin zaben na fidda gwani
  • Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya yi sulhu tsakanin yan takaran da sukayi musharaka a zaben

Kaduna - Babban kotun tarayya dake zamanta a Kaduna ta tabbatar da Sanata Uba Sani a matsayin sahihin dan takaran kujerar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Alkalin kotun, Mohammed Garba, ya yi watsi da karar saboda kotunsa ba tada hurumin sauraron karar, a cewarsa.

Garba ya ce wannan lamarin cikin gida ne tsakanin 'yayan jam'iyya kuma ba matsalar zabe bace, rahton PMNews.

Zaku tuna cewa surukin Shugaban Buhari, Sani Sha'abn, ya shigar da Uba Sani, jam'iyyar APC da hukumar INEC kotu kan zaben fidda gwanin dan takaran gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Sha'aban ya bukaci kotun ta soke zaben saboda an yi magudin Deleget.

Yace tun daga matakin gunduma da karamar hukuma aka sauya sunayen deleget, rahoton NAN.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Uba Sani
Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Sahihin Dan Takaran Gwamnan APC a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Jerin Sunayen Mutum 14 Da Suke Neman Gaje Kujerar Gwamna Malam El-Rufai a 2023

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar gwamnan jihar Kaduna na ƙarshe da zasu fafata a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Jaridar Tribune Online tace sabbin sunayen da INEC ta saki ranar Laraba ya nuna soke tsohon jerin 'yan takara na baya kuma wannan karon kunshin na ɗauke da sunayen 'yan takara da mataimakansu.

Daftarin sunayen ya nuna cewa hukumar zabe ta amince da Jonathan Asake, a matsayin ɗan yakarar gwamnan Kaduna a inuwar Labour Party.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC Ta Saki Jadawalin Yakin Neman Zabenta Na Shugaban Kasa

Daga cikin sunayen yan takara 17 da zasu fafata kan kujerar gwamnan Kaduna sun haɗa da, Sanata Uba Sani (APC), Hon Isah Ashiru Kudan (PDP), da Sulaiman Utsman Hukunyi (NNPP).

Sauran sun haɗa da Hayatudden Lawal Maƙarfi (PRP), Jonathan Asake (LP), Sen. Caleb Zagi (ADC), Dakta Andrew Duya (APGA) da Ibrahim Adamu (SDP) da sauran su.

A wani labarin kuma mun kawo muku Nasihar da Shugaba Buhari Ya Yi Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Wurin Taron Abuja

Shugaba Buhari ya gargaɗi 'yan takarar shugaban kasa 18 su guji kalaman fusata jama'a yayin kamfen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel