Kotu a Amurka Ta Yankewa Hushpuppi Hukuncin Daurin Shekaru 11 a Gidan Yari

Kotu a Amurka Ta Yankewa Hushpuppi Hukuncin Daurin Shekaru 11 a Gidan Yari

  • Kotun Amurka ta yankewa Hushupuppi hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru 11 a kasar
  • An kama Hushpuppi a Dubai, an gurfanar dashi a Amurka bisa laifukan da suka shafi damfara da zamba
  • Abba Kyari, abokin harkallar Hushpuppi na ci gaba da zama a hannun hukumomin Najeriya bisa zargin harkallar kwaya

California, Amurka - Fitaccen dan soshiyal midiya a Najeriya, Roman Abbas da aka fi sani da Hushpuppi ya gamu da hukuncin kotun Amurka, zai yi zaman gidan yari na shekaru 11.

Wannan na zuwa ne a cikin hukuncin da kotun da ke a California ya yanke kan Hushpuppi bisa laifin damfara da sace kudin wani balarabe da sauran jama'a.

Sai dai, Tribune Online ta ruwaito cewa, zai yi zaman shekaru 9 ne a magarkama kasancewar ya yi zaman shekaru biyu kafin a yanke hukuncin.

Kara karanta wannan

Arewa ko Kudu? Peter Obi ya fadi yankin da zai mayar da hankalinsa a kai idan ya gaji Buhari

Kotu ta daure Hushpuppi tsawon shekaru 11 a magarkama
Kotun Amurka Ta Yankewa Hushpuppi Hukuncin Daurin Shekaru 11 a Gidan Yari | Hoto: tribuneonline.com
Asali: UGC

Yadda aka kama Hushpuppi

A 2020, an kama Hushpuppi a kasar Dubai bayan kitsa wata katafariyar damfarar da zai yi a Amurka, Qatar, Burtaniya da suaran kasashe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga nan ne aka zarce dashi Amurka, inda aka gurfanar dashi bisa zargin damfara da sace kudin jama'a.

Ya amsa laifinsa na hada baki wajen aikata damfara tare da mutane da dama a ciki da wajen Amurka.

Ya samu hukuncin shekaru 11 ne a hannun mai shari'a Otis Wright bayan da ya nemi a yi masa sassauci bayan sakin jiki da ayyukan share-share da goge-goge a magarkama.

Makomar shafin Instagram na Hushpuppi

Ku sani cewa, shafin Instagram na Hushpuppi mai mabiya 2.8 ya zama tarihi, ya kuma disashe daga idon jama'a.

Sai dai, ba san ko Instagram ne ya cire shafin ba, ko kuma wani ne ya sauke shafin gaba daya daga kafar.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

A bangare guda, GhanaWeb ta ruwaito cewa, kamfanin Instagram ya datse shafin Hushpuppi ne saboda saba wasu ka'idoji da dama.

Abba Kyari Ya Magantu Kan Kadarori 14 Da FG Ta Bankado A Matsayin Nasa

A wani labarin, dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari, ya karyata batun mallakar kadarori 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado.

Kyari ya ce sabanin rahoton cewa an gano makudan kudade a asusun bankinsa, naira miliyan 2.8 ne kacal a asusunsa na UBA da kuma wani N200,000 a asusunsa na Sterling, jaridar Leadership ta rahoto.

A cewar wata sanarwa daga lauyansa, Barista Hamza Dan Tani, duk zarge-zargen da NDLEA ke yi dangane da kudade da kadarori mallakar Abba Kyari karya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel