Gobara Ta Kama Hedkwatar Hukumar NYSC Dake Birnin Tarayya Abuja

Gobara Ta Kama Hedkwatar Hukumar NYSC Dake Birnin Tarayya Abuja

  • Da sanyin safiyar Juma'a wuta ta kama wani bangare na Yakubu Gowon, hedkwatar hukumar NYSC
  • Mai magana da yawun hukumar ya bayyana cewa ba'a asarar komai ba sakamakon wannan gobara
  • Ya jinjinawa jami'an kashe wutan birnin Abuja bisa saurin zaburarsu wajen kashe wutar

FCT - Gobara ta ci bal-bal a hedkwatar hukumar bautar kasa na matasa da suka kammala karatun gaba da sakandare watau NYSC ranar Juma'a, a birnin tarayya Abuja.

Diraktan yada labaran hukumar, Eddy Megwa, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Ya tabbatar da cewa gobarar ta auku da safiyar Juma'a misalin karfe 7:30 amma ya ce ba'a yi rashin rai ba, kamar yadda ya daura a shafin Tuwita.

A cewarsa, jami'an kwana-kwanan birnin tarayya cikin gaggawa suka kashe wutar.

Yace:

Kara karanta wannan

Jami’an NDLEA na Fuskantar Barazana da Kisa daga Dillalan Kwayoyi, Marwa

"Mun yi sa'a babu rashin rai kuma an samu kwashe dukkan takardu masu amfani."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hukumar na godiya ga jami'an kwana-kwanan Abuja bisa amsa kiran da suka yi kan lokaci."

Gobarar ta shafi tsauni na 3 ne inda ofishohin sashen shirye-shirye, bincike da lissafi yake kuma daki daya kadai ya ci wuta,riwayar Dailytrust.

NYSC Headquaters
Gobara Ta Kama Hedkwatar Hukumar NYSC Dake Birnin Tarayya Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel