Ado Doguwa: Ban Yi Barazanar Tona Wa Ganduje Asiri Ba, Shugaba Na Ne

Ado Doguwa: Ban Yi Barazanar Tona Wa Ganduje Asiri Ba, Shugaba Na Ne

  • Honarabul Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya ya karya rahoton cewa ya yi barazanar tona wa Gwamna Ganduje na Kano asiri
  • Doguwa ya fitar da sanarwa yana mai cewa ya umurci lauyoyinsa su tuntubi kafar watsa labarai na intanet da ta wallafa labarin ta janye kuma ta nemi afuwarsa
  • Dan majalisar tarayyar ya jinjinawa Gwamna Ganduje inda ya ce shugabansa ne kuma mai bashi shawara a harkokin rayuwa kuma yana alfahari da nasarorinsa a jihar Kano

Kano - Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya nesanta kansa daga wani rahoto da kafar watsa labarai na intanet ya wallafa na cewa ya yi barazanar tona Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano kan cire kudi daga albashin ma'aikatan kananan hukumomi a jihar, yana mai cewa labarin karya ne, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

Doguwa, cikin sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannunsa, ya ce Ganduje har yanzu shugabansa ne yana mai cewa rahoton da mikiyawww.hausanewsnigeriya ba gaskiya bane.

Ado Doguwa
Ado Doguwa: Ban Yi Barazanar Tona Wa Ganduje Asiri Ba, Shugaba Na Ne. Hoto: Vanguard.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Doguwa ya bayyana rahoton a matsayin 'tsantsagwaron karya, makirci, da labarin karya' da makiya 'masu hassada' suka yi don bata masa suna da janyo rudani tsakaninsa da 'shugabansa kuma bada shawara', Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Lauyoyi na za su dauki mataki kan lamarin

Doguwa, shahararren dan majalisa ya ce lauyoyinsa za su dauki mataki a kan lamarin, yana mai cewa bai taba yin wani mummunan zato ga gwamnan ba, wanda ya bayyana a matsayin gwamna 'mafi kwazo a jihar, ballanta ya yi maganar tona shi."

Doguwa ya ce yana cikin gwamnatin Ganduje wanda ya ce duk wani mutum mai tunani na gari a jihar zai yi alfahari da shi wanda ya kawo cigaba a dukkan bangarorin cigaban rayuwa, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Dan majalisar ya bukaci mawalafin labarin ya janye labarin ya kuma nemi afuwarsa, rashin hakan zai janyo ya dauki na shari'a.

Wani sashi na kalamansa:

"Ba gaskiya ba ne na yi wa mahaifinmu gwamnan jihar mu Kano, kuma jagoran jam’iyyarmu ta APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ne jagorana na har abada barazana, kan albashin ma’aikata kamar yadda kafar yada labarai ta intanet ta wallafa.
"Na umurci lauyoyi na su rubuta wa mawallafin ya janye labarin mara tushe, ya nemi afuwa daga gare ni, kuma ya bayyana majiyarsa, rashin hakan zai janyo daukan mataki na shari'a."

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yi gargadin cewa idan har manyan APC basu dauki cikakkiyar iko kan jam’iyyar ba a jihar Kano, toh za su iya shank aye a zaben 2023, jaridar Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Doguwa na so Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbi ragamar kula da harkokin jam’iyyar mai mulki don duba yadda tsohon kwamishinan harkokin kananan hukumomi kuma dan takarar mataimakin gwamnan APC, Murtala Garo ke wuce gona da iri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel