Peter Obi Yayi Alkawarin Mayar da Hankalinsa Kan Yankin Arewa Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Peter Obi Yayi Alkawarin Mayar da Hankalinsa Kan Yankin Arewa Idan Ya Zama Shugaban Kasa

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour ya yi alkawarin amfani da albarkar kasar noma da Allah ya yiwa Arewa wajen amfanar da kasar nan
  • Tsohon gwamnan na Anambra ya ce zai zuba kudaden Najeriya a yankin Arewa don habaka fannin noma
  • A fahimtarsa, yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ci gaban Najeriya shi ne babban abin da ya fi mai da hankali a kai

Najeriya - A wani batu mai daukar hankali, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana cewa, zai yi duk mai yiwuwa wajen amfani da albarkar da Allah ya ajiye ta kasar noma a Arewacin Najeriya don ci gaban kasa.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust ta wallafa, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Peter Obi ya ce zai mai da hankalinsa ga Arewa idan ya gaji Buhariu
Peter Obi Yayi Alkawarin Mayar da Hankalinsa Kan Yankin Arewa Idan Ya Zama Shugaban Kasa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewarsa, yankin Arewacin Najeriya na da kasar noma mai girma, inda ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta zuba hannun jari a fannin.

Abin da Peter Obi zai yi idan ya gaji Buhari

Ya shaidawa Daily Trust cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna da kasa mai girma a Arewa da idan aka zuba hannun jari kuma aka noma ta yadda ya dace, Najeriya za ta sauya.
"Adadin mutanen da ya cire daga talauci, adadin wadanda zan raba da batun aware, kuma shi ne adadin da zan rage na ta'addanci.
"Zan gana da mutane a Arewa, zan gana da mutane a ko'ina sannan na ce su zo, mu zama ahali. Ina son 'yan Najeriya su yi alfahari da cewa su 'yan Najeriya ne.
"Abin da muke dashi a yanzu shine, muna da kasa mai suna Najeriya, amma ba mu da 'yan Najeriya. Ina so na dawo da 'yan Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya fadi wadanda zai siyarwa matatun man Najeriya idan ya gaji Buhari

Zan Sayar da Matatun Mai Ga ’Yan Kasuwa Idan Na Gaji Buhari, Inji Atiku

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana manufarsa ta siyar da matatun mai Najeriya ga 'yan kasuwa idan aka zabe a 2023.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da gidan rediyon Amurka (VOA Hausa) a ziyarar da ya kai birnin Washington DC ta kasar Amurka.

Ya bayyana cewa, matsayarsa game da batun siyar da matatun mai ba sabon lamari bane, domin a cewarsa ya sha fadin inda ya dosa, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel