Latest
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa jakadan ƙasar a Burtaniya kiranye, ya umarci ya tafi hutun watanni biyu kuma ya gode masa bisa aikin da ya yi.
Hankula sun tashi bayan wani basarake ya tilasta matasa sun saki matan ƴam bindigan da suka kama a jihar Zamfara bayan sun sace musu mutum shida A ƙauyensu.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto ya amince da sakin kudi kimanin naira biliyan 4 don siyan kayan abinci da za a raba a fadin kananan hukumomin jihar.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa ya ji dadin abun da ya faru a Gabon bayan sojoji sun kwace mulki a kasar mai arzikin man fetur.
Wani dan Najeriya a kasar Birtaniya ya makale bayan matarsa da ke cin amanarsa ta soke bizarsa. An ba shi wa’adi ya gyaro lamarin ko a kore shi gida Najeriya.
Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, ya bayyana hukuncin da zai ɗauka kan waɗanda suka karkatar da kayayyakin tallafi waɗanda gwamnatin tarayya ta bayar.
Kasurgumin dan daba da ake nema ruwa a jallo, Sadiq da aka fi sani da 'Big Star' a Kano ya shiga hannu bayan kama shi ya ji wa wani dattijo rauni da makami.
Matasa a jihar Zamfara sun yi garkuwa da matan 'yan bindiga a yankin Birnin Magaji, sun sha alwashin cewa ba za su sake su ba har sai an sake musu 'yan uwa.
Kamfanin BUA karkashin jagorancin biloniya, Abdussamad Rabiu ya shirya rage farashin siminti a fadin Najeriya baki daya don bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Masu zafi
Samu kari