“An Ba Ni Su Kyauta”: Dan Najeriya Ya Tsinci iPads 500 a Shagon da Yake Aiki

“An Ba Ni Su Kyauta”: Dan Najeriya Ya Tsinci iPads 500 a Shagon da Yake Aiki

  • Wani dan Najeriya ya taki sa’a yayin da ya tsinci wasu wayoyi kirar iPads guda 500 a shagon da yake aiki a kasar waje
  • A cewar mutumin, ya kai rahoton tsintar wayoyin ga manajan shagon, amma shugaban ya ba shi umarnin ya yi amfani da su
  • Mutumin ya walafa labarin a shafinsa na X, yana tambayar mutane ko akwai wadanda suke so ya tura masu wayoyin don ba 'ya'yansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani dan Najeriya da ke aiki a wani shago a kasar waje ya yi gamo da katar da wasu wayoyi kirar iPads wadanda ke ajiye a shagon na tsawon lokaci.

Ko da ya dauke su ya kai wa shugaban shagon, sai ya cika da mamaki da kuma farin ciki yayin da manajan ya ba shi damar mallakarsu gaba daya.

Kara karanta wannan

Duk da gwamnati ta dauki mataki, farashin gas din girki ya sake lulawa har ya haura N1300

Matashi ya tsinci iPads a wurin aikinsa.
Matashin ya ce zai bai wa mutane kyautar wasu daga cikin iPads din. Hoto: X/@EronsJohnson.
Asali: Twitter

Ya ce akwai a kalla iPads guda 500 da ya tsinta a cikin shagon, kuma ya wallafa hotunan wasu daga cikinsu a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin zai yi kyautar da iPad

Mutumin mai suna Dokta Fames, ya tambayi mabiyansa na shafin X ko suna da bukatar ya basu kyautar wasu daga cikin iPads din domin su ba 'ya'yansu.

A cewarsa:

"Na shiga cikin wani tsohon daki a shagon da na ke aiki domin kwashe kayan datti, kwatsam sai na tsinci iPads guda 500. Manajan wajen ya ce ya ba ni su kyauta.
"Duk da cewa wasu sun tsufa, wasu kuma ina kokarin na kunnasu, amma akwai farin ciki a yadda ya mallaka mani su ganin cewa zubar da su za mu yi a bola."

Mutane da dama sun nuna sha'awar samun iPads din don mallaka wa 'ya'yansu.

Kara karanta wannan

"Ka canja mani rayuwa": Bature ya bai wa dalibin Najeriya naira miliyan 159 da sabuwar mota

Dubi sakonsa a kasa:

iPad: Abin da mutane ke cewa

@Solomon_Buchi ya ce:

"Zan iya samun guda biyu? Na gode!!!!"

@SoniaUzama ta ce:

“Don Allah ka tabbata ka samu izininsa a rubuce, ko ka aika masa sakon imel na godiyar mallaka maka su da ya yi, kayi hakan don tsira da mutuncinka nan gaba."

@mrboboskie ya ce:

"Zan ji dadi idan zan iya samun guda daya."

Bidiyon adaidaita sahu mai abun mamaki

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo maku rahoton wani adaidaita sahu, da aka yi wa ado na jan hankali, wanda kuma aka saka masa talabijin, fanka da kujeru masu laushi.

Mutane da dama sun jinjinawa fikirar mai adaidaita sahun na yadda ya kawata keke-napep dinsa, bayan da wani fasinja ya dauki bidiyon keken ya wallafa a shafin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel