Batun Ba Dalibai Rance Ya Bi Ruwa: Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da Shirin Aron Kudin Karatu

Batun Ba Dalibai Rance Ya Bi Ruwa: Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da Shirin Aron Kudin Karatu

  • Gwamnatin tarayya ta ɗage ƙaddamar da shirin ba ɗaliban Najeriya rancen kuɗi har sai abin da hali ya yi
  • Sakataren NELFUND, Dr. Akinwunmi Sawyer shi ne ya bayyana hakan a yayin da ake wata tattaunawa da shi
  • Sawyer ya bayyana cewa an ɗage ƙaddamar da shirin ne saboda wasu ƴan gyare-gyare da ake buƙatar a yi kafin a fara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ɗage ƙaddamar da shirin bayar da lamuni ga ɗaliban Najeriya har sai baba ta gani.

Akintunde Sawyer, babban sakatare na asusun bada lamuni na Ilimi a Najeriya (NELFUND), ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise News.

Kara karanta wannan

Sanata Ningi ya yi murabus daga mukaminsa, ya ambaci dalili

An dage kaddamar da shirin ba dalibai lamuni
Gwamnatin Tinubu ta dage kaddamar da shirin ba dalibai lamuni Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Gwamnatin Tinubu za ta ba ɗalibai lamuni

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar ne a watan Yunin 2023, domin kafa asusun lamuni na ɗalibai (SLF), wanda zai bada lamuni mara ruwa ga ɗaliban Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙudurin wanda Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai ne ya gabatar, an shirya fara aiwatar da shi ne a tsakanin watan Satumba da Oktoba 2023.

Bayan gaza fara gudanar da shirin kamar yadda aka tsara da farko, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa za a fara shirin a watan Janairun 2024.

Daga baya Sawyer ya bayyana cewa za a ƙaddamar da shirin a cikin watan Maris, 2024.

Meyasa aka ɗage ƙaddamar da shirin?

Sai dai, ƙasa da sa'o'i 48 kafin ƙaddamar da shirin, Sawyer ya ce an ɗage shirin bayar da rancen saboda wasu gyare-gyare da za a yi kafin ƙaddamar da shi.

Kara karanta wannan

Ramadan: Shugaban majalisa ya fadi abin da Najeriya ta fi bukata a lokacin azumi

A kalamansa:

"Abin takaici, ba zan iya bayar da wani takamaiman lokaci ba. Muna jira domin tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki sun haɗa kai don tabbatar da cewa ba wanda aka bari a baya,
sannan za mu iya aiwatar da wannan shirin cikin hanyar da ta dace."

ASUU na adawa da ba ɗalibai rance

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta yi suka a kan wannan shiri na ba ɗalibai rancen kuɗi.

Ƙungiyar ta reshen jihar Bauchi ta bayyana cewa ba aron kudi ɗaliban Najeriya ke buƙata ba, tallafi mai kyau ya kamata a ba su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel