Ningi: Jerin Sanatocin Najeriya da Aka Dakatar Daga 1999 Zuwa 2024 da Kuma Dalilin da Ya Sa

Ningi: Jerin Sanatocin Najeriya da Aka Dakatar Daga 1999 Zuwa 2024 da Kuma Dalilin da Ya Sa

  • A yayin da majalisar dattawa ta sanar da dakatar da Sanata Abdul Ningi, Legit ta kawo jerin 'yan majalisar da hakan ta taba faruwa a kansu
  • An dakatar da Ningi, jigo a jam’iyyar PDP yayin zaman majalisar na ranar Talata, bayan yayi zargin cewa an yi cushe a kasafin kudin 2024
  • Akalla sanatoci bakwai ne tarihi ya nuna majalisar dattawa ta dakatar da su bisa wasu laifuka daban-daban da suka aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A ranar Talata ne majalisar dattawan Najeriya ta sanar da dakatar da Sanata Abdul Ningi bayan da ya yi zargin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi cushe a kasafin kudin 2024.

Sai dai kafin dakatar da shi, an taba dakatar da wasu sanatocin Najeriya a zauren majalisar dattijai bisa wasu laifuka daban-daban da suka aikata.

Kara karanta wannan

Abdul Ningi: Gwamnan PDP a Arewa ya nuna goyon bayansa ga sanata, ya fadi matakin da zai dauka

Majalisar dattawa ta dakatar da Ndume, Ningi da sanatoci 3
A 2000 ne majalisar dattawa ta fara dakatar da Sanata Joseph Waku. Hoto: Ali Ndume, Abdul Ningi
Asali: UGC

The Cable ta kawo muku cikakkun jerin sanatocin da aka dakatar a zauren majalisar dattawan da kuma dalilin dakatar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Femi Okurounmu (Ogun ta tsakiya) - 1999

A shekarar 1999 ne aka dakatar da Sanata Femi Okurounmu daga mazabar Ogun ta tsakiya bisa wani ikirari da ya yi na cewa wasu sanatoci na shirin tsige Olusegun Obasanjo.

2. Joseph Waku (Benuwai ta Arewa maso Yamma) - 2000

A shekarar 2000 ne aka dakatar da Sanata Joseph Kennedy Waku na jam'iyyar PDP daga mazabar Benuwai ta Arewa maso Yamma daga zauren majalisar.

Waku dai ya janyo cece-kuce a lokacin da ya ce gara sojoji su dawo mulki ta hanyar juyin mulki da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ci gaba da mulkin kama-karya.

Tsohon Sanatan ya ce gwamnatin Obasanjo ita ce mafi muni da Najeriya ta taba samarwa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sanata Ningi: Tinubu ya sanya labule da shugabannin majalisa, bayanai sun fito

3. Arthur Nzeribe (Mazabar Orlu, Imo) - 2002

A watan Nuwambar 2002, shugaban majalisar dattawa Anyim Pius Anyim ya dakatar da Sanata Arthur Nzeribe (daga mazabar Imo) na har abada saboda zargin damfarar Naira miliyan 22.

An ruwaito cewa Nzeribe ya shirya wata makarkashiya ta tsige shugaban majalisar dattawa na wancan lokacin, Anyim.

Majalisar dattawan ta kuma zartas da kuduri na baki daya, inda ta mika lamarin Nzeribe ga ‘yan sanda domin gudanar da cikakken bincike.

4. Isah Mohammed (Neja ta tsakiya) - 2004

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, a watan Oktoba, 2004 ne aka dakatar da Sanata Isah Mohammed (daga mazabar Neja ta tsakiya), bisa samun shi da laifin zabga wa Sanata Iyabo Anisulowo mari a bainar jama'a.

5. Ali Ndume (Borno ta Kudu) - 2017

A shekarar 2017, Majalisar Dattawa ta dakatar da Ali Ndume (daga mazabar Borno ta Kudu) bayan ya nemi a gudanar da bincike kan zargin shigo da wata mota kirar Range Rover mai kariyar harsashi.

Kara karanta wannan

Ningi: Majalisa ta dauki mataki kan Sanatan da yayi zargin cushen N3tr a Kasafin 2024

Ndume ya yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa na wancan lokacin Bukola Saraki da kuma Dino Melaye na karya na da hannu wajen shigo da motar ba bisa ka'ida ba.

An dakatar da shi na tsawon watanni shida, maimakon shekara guda da kwamitin da'a ya ba da shawara.

6. Ovie Omo-Agege (Delta ta tsakiya) - 2018

A shekarar 2018, aka dakatar da Sanata Ovie Omo-Agege, mai wakiltar Delta ta tsakiya na tsawon kwanaki 90 daga zaman majalisar.

Kwamitin majalisar mai kula da kararrakin jama’a da da’a ne ya binciki Omo-Agege kan kalamansa na sake tsara jadawalin zabe, inda ya ba da shawarar dakatar da shi.

A cewar rahoton, dan majalisar wanda ya yi wannan katobara ya shaida wa kwamitin cewa tuni ya shigar da karar lamarin gaban kotu.

Sai dai kuma shugaban majalisar dattawa na lokacin, Olubukola Saraki, ya dage kan cewa dole ne a ladabtar da Omo-Agege domin ya zama izina ga 'yan baya.

Kara karanta wannan

An hargitse a Majalisa kan zargin Sanata Ningi, an fifita manyan Sanatoci wurin rabon kudi

7. Abdul Ningi (Bauchi ta tsakiya) - 2024

A ranar Talata, 12 ga watan Maris, 2024 ne majalisar dattawan Najeriya karkashin jagorancin Godswill Akpabio ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ta tsakiya.

An dakatar da Ningi, jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yayin zaman majalisar na ranar Talata, bayan yayi zargin cewa an yi cushe a kasafin kudin 2024.

Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi

Idan ba a manta ba, Sanata Ningi, a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC a ranar Asabar, ya yi zargin cewa majalisar tarayya ta yi cushe a kasafin kudin 2024 da Naira tiriliyan 3.7.

Sanatan Bauchi ta tsakiya ya kuma yi ikirarin cewa kasafin kudin shekarar 2024 ya kai N25tn yayin da wanda fadar shugaban kasa ke aiwatarwa ya kai N28.7tn.

Ningi: Tinubu ya gana da Akpabio

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio jum kadan bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi.

Dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Ningi ya biyo bayan amincewar mafi rinjayen sanatoci sakamakon kalaman Ningi na cewa 'yan majalisar sun yi cushe a kasafin 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel