Fasinjoji da Dama Sun Bace Yayin da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Wata Mota a Taraba

Fasinjoji da Dama Sun Bace Yayin da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Wata Mota a Taraba

  • Wasu mutane ɗauke da makamai da ake zargin ƴan banga ne sun kai farmaki kan wata motar bas a jihar Taraba
  • A yayin harin da miyagun suka kai, an nemi mutum 15 waɗandansuka haɗa da mata da yara daga cikin fasinjojin motan an rasa
  • Shugaban ƙaramar hukumar Donga ta jihar ya tabbatar da aukuwar lamarim inda ya ce suna ci gaba da neman mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Fasinjoji 15 da suka haɗa da mata da yara ne suka ɓace a wani hari da aka kai kan wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 a jihar Taraba.

Jaridar Leadership ta ce an kai hari kan motar ne wace ta taso daga Zaki/Biam a jihar Benuwai zuwa Maihura a ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba, a ranar Talata, 11 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Batun ba dalibai rance ya bi ruwa: Gwamnatin Tinubu ta dakatar da shirin aron kudin karatu

'Yan bindiga sun kai hari a Taraba
'Yan bindiga sun farnaki fasinjohi a jihar Taraba Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ana zargin dai wasu ƴan banga ɗauke da makamai ne suka kai wa motar hari a ƙauyen Gamkwe da ke Maraban-Baisa a ƙaramar hukumar Donga ta jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Direban motar, Mista Mpuuga Mbaave wanda ya samu ya tsere ɗauke da raunuka, ya ce ƴan bangan na ɗauke da mugayen makamai da suka haɗa da bindigogi, adduna da sauran ƙananan makamai.

A kalamansa:

“Na ɗauko fasinjohi 18 daga Zaki/Biam. Muna wuce Maraba, sai na hango mutane masu yawa a cikin kayan ƴan banga, sai na ji a jikina cewa akwai matsala.
"Sai na tsaya amma sai wani daga cikin mutanen ƙauyen ya ce mani na wuce kawai wasu ƴan banga mutum biyu ne masu garkuwa da mutane suka kashe, shi yasa suka taru, don haka babu matsala na wuce kawai.
"Yayin da na matsa kusa da su, wasu daga cikin ƴan bangan sai suka fara cewa ku kashe su. Mutanensu ne suka kashe mana mutane, sai suka fara farmakar fasinjojin da ji musu raunuka da adduna."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama hatsabiban masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a Arewa

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Shugaban ƙaramar hukumar Donga, Hon Ezra Voka, ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da jaridar Leadership ta tuntuɓe shi.

A kalamansa:

"Ina cikin daji yanzu haka muna neman mutanen da suka ɓace, ba zan iya cewa komai ba har sai na samu cikakkun bayanai tukunna."

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

'Sai an ba mu N40tr' - Ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindigan da suka sace wasu mutane a jihar Kaduna sun bayyana maƙudaden kuɗaɗen da za a ba su a matsayin kuɗin fansa.

Miyagun sun bayyana cewa sai an ba su N40tr da motocin Hilux guda 11 kafin su sako mutum 16 da suka sace a ƙauyen Gonin Gora.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel