Latest
Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya shawarci Alhaji Yahaya Bello da ya daina wasan buyan da yake yi, ya fito ya kai kansa ga hukumar EFCC.
Kwamitin binciken shari'a da gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kafa, zai fara zamansa domin binciken gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Kungiyar 'Concerned North-Central APC Stakeholders' ta nesanta kanta daga zanga-zangar neman tsige Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC.
Al-Masaakin wata gidauniya ce da ta tallafawa marasa karfi yayin Ramadan. A rahoton nan, mun kawo hirar da aka yi game da kokarin Al-Masaakin a jihohin Najeriya
Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan hadiminsa a bangaren kwadago, Kwamred Muhammad Adam Erena bayan rasuwarsa a yau Lahadi.
Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe daya daga cikin kodinetocin yakin zaben gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a kofar gidansa da ke Akoko.
An bude gidan wasan dabe da raye-raye na farko a cibiyar al'adu ta Sarki Fahad da ke a birnin Riyadh inda aka kaddamar da wasan dabe na Zarqa Al Yamama.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'addan da suka addabi mutane a jihar Neja. An hallaka tsagerun tare da lalata maboyarsu.
Sarkin Dubai ya amince da kashe Naira tiriliyan 43 domin gina sabwar tashar jirgin saman Al Maktoum. Idan an kammala aiki, filin jirgin zai zamo mafi girma a duniya.
Masu zafi
Samu kari