Ondo: An Kashe Kodinetan Yaƙin Neman Zaben Gwamnan APC, ’Yan Sanda Sun Magantu

Ondo: An Kashe Kodinetan Yaƙin Neman Zaben Gwamnan APC, ’Yan Sanda Sun Magantu

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe Alaba Excel Abbey a kofar gidansa da ke Supare Akoko
  • Alaba Excel Abbey, na daya daga cikin masu gudanar da yakin neman zaben gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo
  • Jami’iar hulda da jama’ata ‘yan sandan jihar (PPRO), Funmilayo Odunlami-Omisanya ta ce rundunar ta kaddamar da bincike kan kisan gillar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ondo - An kashe Alaba Excel Abbey, daya daga cikin masu gudanar da yakin neman zaben gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo.

Mista Abbey, wanda shi ne kodinetan unguwanni na kungiyar yakin zaben Aiyedatiwa (LACO-SF), an kashe shi ne a gidansa da ke Supare Akoko a da ke Akoko ta Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Cikakken sakamako: PDP ta lashe zaben dukan kujerun kananan hukumomi 33 a jihar Oyo

'Yan bindiga sun kashe kodinetan yaƙin zaben Gwamna Lucky Aiyedatiwa
An kashe kodinetan yaƙin zaben Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a kofar gidansa. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Asali: Twitter

Yadda aka kashe kodinetan Aiyedatiwa

Jaridar Daily Trust ta samu labarin cewa marigayin shi ne jami’in jam’iyyar APC (RO) a mazabar 'Ward 10' a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka kammala kwanan baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani kanin marigayin, Mista Samuel Abbey, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa an harbe dan siyasar ne a kofar gidansa.

A halin da ake ciki, kungiyar yakin zaben Lucky Aiyedatiwa (LACO-SF) ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Mista Abbey.

Rundunar 'yan sanda ta magantu

Kungiyar ta kuma yi kira ga jami’an tsaro musamman jami’an ‘yan sanda da su kare ‘ya’yanta daga irin wadannan munanan hare-hare, rahoton jaridar Leadership.

Jami’iar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takarar gwamna da zai kara da Aiyedatiwa

Funmilayo Odunlami-Omisanya ta ce rundunar ‘yan sandan jihar ta kaddamar da bincike kan kisan gillar.

Ajayi Agboola: Dan takarar PDP a Ondo

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta tsayar da Mr. Ajayi Agboola a matsayin dan takararta a zaben gwamnan jihar Ondo mai zuwa.

Mr. Ajayi Agboola wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar ne ya samu rinjaye a kan abokan karawarsa a zaben fidda gwani da PDP ta gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel